Ba a Rubuta Kundin Tsarin Mulkin Najeriya Cikin Natsuwa Ba, Shugaban Majalisa
- Shugaban majalisar wakilai a Najeriya ya bayyana bukatar a sauya kundin tsarin mulkin Najeriya
- Ya bayyana cewa, ba a rubuta kundin tsarin cikin natsuwa ba, wannan yasa ake da matsaloli da yawa
- Ya bukaci hadin kan 'yan Najeriya da goyon bayansu kan aikin sauya kundin tsarin mulkin kasar
Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya gaza magance wasu manyan matsaloli da ke addabar kasar, abin da ya sa kenan 'yan majalisa suka yanke shawarin sauya shi, BBC Hausa ta ruwaito.
Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wajen taron jin ra'ayoyin jama'a kan sauya kundin tsarin mulkin a Legas a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa majalisar wakilan shawara kan yada labarai ta fitar.
Shugaban majalisar ya ce kundin tsarin mulki ba wai tushen kasa ba ne kawai, kamata ya yi ya zayyana ka'idojin zaman kasa da kuma burikanta na akida da gaskiya, amma "namu kundin tsarin mulkin na cike da nakasu," a cewar Gbajabiamila.
KU KARANTA: El-Rufai Ya Sake Sabbin Nadi a Gwamnatinsa, Ya Yi Garanbawul a Wasu Wurare
Ya ce dalilan da suka janyo hakan kuwa har da yadda aka yi gaggawar samar da kundin tsarin mulkin na 1999 don ganin an mayar wa farar hula mulki bayan shafe gomman shekaru karkashin mulkin soja.
Sai dai ya ce a wannan karon Majalisar Dokokin za ta iya yin nasarar cimma burin sauya kundin ne kawai idan har 'yan kasa suka mara wa kokarinta baya tare da ba da gudunmowarsu.
Rueben Abati ya ruwaito shi yana cewa:
“A koda yaushe niyyar mu ita ce wata rana a matsayin mu na mutane daya kuma al’umma daya, mu gyara wannan kundi ta yadda zai bayar da amsa ga bukatun mutanen Najeriya tare da bayyana dalla-dalla yadda za mu yi niyyar cimma burin da muke da shi ga al'ummarmu."
KU KARANTA: Bamu da Kudirin Zarcewa a Kan Mulki, INEC Zata Gudanar da Zaɓen 2023, Shugaba Buhari
Ya ce duk masu wannan mummunan aiki su sani, yana sane kuma nan ba da dadewa ba za su sha kunyar abubuwan da suke aikatawa.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ta shafin Tuwita, wanda Legit.ng Hausa ta gano a yau Talata 1 ga watan Yuni.
Asali: Legit.ng