Gwamnonin kudu maso gabas sun nemi a kama wadanda ke da alhakin kashe Gulak

Gwamnonin kudu maso gabas sun nemi a kama wadanda ke da alhakin kashe Gulak

- Kungiyar gwamnonin kudu maso gabas ta fitar da sanarwa inda ta soki kisan Ahmed Gulak a jihar Imo a ranar Lahadi, 30 ga Mayu

- Gwamnonin da ba su ji dadin abin da ya faru ba sun bayyana dalilin da ya sa yake da muhimmanci a kame wadanda ke da alhakin kisan

- A gefe guda, an danganta mutuwar Gulak da rashin tsaro a yankin kudu maso gabas, yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin kisan gillar siyasa

Gwamnoni daga yankin kudu maso gabashin kasar sun yi Allah wadai da kisan Ahmed Gulak, wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Gwamnonin sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su hanzarta kamo wadanda ke da alhakin kisan dan siyasar.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2023: Babban limami zai shiga tseren neman kujerar gwamna a Adamawa

Gwamnonin kudu maso gabas sun nemi a kama wadanda ke da alhakin kashe Gulak
Gwamnonin kudu maso gabas sun nemi a kama wadanda ke da alhakin kashe Gulak Hoto: @realdaveumahi
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi na Ebonyi ya fitar a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, bayan ganawar sirri kan matsalar tsaro a yankin.

Umahi ya ce:

"Cike da kaduwa muka samu labarin mutuwar Alhaji Ahmed Gulak a hannun 'yan bindigan marasa azanci."

KU KARANTA KUMA: Jama’a na cece kuce yayinda aka tsara katin gayyatar aure kamar takardar kudi N500

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa gwamnonin sun jajantawa dangin Gulak da gwamnatin jihar Adamawa kan kisan dan siyasan.

Sun tabbatarwa da takwarorinsu na yankin arewa kudurinsu na gano lamarin da ke kewaye da mutuwar Gulak.

Kungiyar ta bukaci jama'a da su nuna dattako tare da baiwa hukumomin tsaro damar ci gaba da binciken su.

A wani labarin, mai girma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce masu kai wa jami’an tsaro da wasu wuraren hari a yankin Kudancin kasar nan mutanensu ne.

David Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, an yi magana da gwamnan ne ta kafar yanar gizo a jiya.

Da yake zanta wa da manema labarai a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, 2021, gwamnan ya koka a kan yadda mutanen yankinsa suke faman tada zaune-tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel