Gwamna ya fasa kwai, ya tona asirin masu tada zaune tsaye a jihohin Kudancin Najeriya

Gwamna ya fasa kwai, ya tona asirin masu tada zaune tsaye a jihohin Kudancin Najeriya

- Gwamna David Umahi ya ce ya san wadanda suke kai hare-hare a yankin Kudu

- David Umahi yake cewa matasan Ibo ne suke wadannan mugun aiki ba kowa ba

- Gwamnan na Ebonyi ya yi kira ga matasan da su guji jefa kansu a cikin hallaka

Mai girma gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya ce masu kai wa jami’an tsaro da wasu wuraren hari a yankin Kudancin kasar nan mutanensu ne.

David Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, an yi magana da gwamnan ne ta kafar yanar gizo a jiya.

Da yake zanta wa da manema labarai a ranar Talata, 1 ga watan Yuni, 2021, gwamnan ya koka a kan yadda mutanen yankinsa suke faman tada zaune-tsaye.

KU KARANTA: Rashin tsaro: PDP ta jefa mu a halin da ake ciki - APC

Gwamna David Umahi ya ce ba kowa suke wannan ta’adi ba face haifaffun matasan kasar Ibo.

A cewar gwamnan, matasan da ake ganin cewa sune manyan gobe, sun dauki makamai, suna kai hare-haren da suka jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Gwamna Umahi ya gargadi matasan da ake hada kai da su ana wannan mummunan aiki su tuba, domin su ne a wata rana kasar zai koma a hannunsu.

Ga abin da gwamnan yake cewa:

KU KARANTA: APC ta ba ‘Dan Majalisa hakuri, ta soke dakatar da shi da aka yi

Gwamna ya fasa kwai, ya tona asirin masu tada zaune tsaye a jihohin Kudancin Najeriya
Gwamna Dave Umahi Hoto: @EbonyiGov
Asali: UGC

“Mutanenmu su fito su yi magana, su bayyana cewa ‘yan bindigan nan da ake cewa ba a san su ba, ba boyayyu ba ne, matasan mu ne, maza da mata.”

Ya ce: “Su ne wadanda za su kare kasar mu wata rana; su daina mika wuya inda za a hallaka su.”

Punch ta ce a matsayinsa na shugaban gwamnonin Kudu maso gabas, ya yi kira ga gwamnatin jihar Benuwai ta kirkiri jami’an tsaro da su kare al’umma.

A ranar Talatar nan ne aka ji cewa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ziyarci babbar hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke jiharsa.

Gwamnan ya roki jami’an tsaron su aiwatar da umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada na harbe duk wani mutumi da aka samu dauke da bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel