Wata Sabuwa: Mijin Aljana Ya Bayyana Gaskiyar Lamarinsa Na Auren Aljana

Wata Sabuwa: Mijin Aljana Ya Bayyana Gaskiyar Lamarinsa Na Auren Aljana

- Mijin aljana ya bayyana gaskiyar abinda ke tsakaninsa da aljana da ya yi ikirarin ya aura a baya

- Ya bayyana karara cewa, babu wani batun aljana, karyane kawai don ya samu kudin kashewa

- Ya kuma ce, mahaifiyarsa ce ke da larura

A wani bidiyo da ya shahara a kafafen sanda zumunta, an ga wani mutum da ya yi ikirarin cewa ya auri aljana kana ya hada ta da matarsa mutum suke zaune a gida daya.

Mijin aljana, wato Malam Ahmadu Ali Kofar Na'isa, ya bayyana wasu abubuwan ban al'ajabi a baya, yayin da yake bayyana yadda yake mu'amalantar matarsa aljana duk da cewa halittarsu daban.

A wani bidiyon, har bayani ya yi na yadda yake cire kudade daga asusun ajiyar aljanu, wanda yake bashi damar cire kudaden Najeriya da wani katin ATM da yake dashi na musamman.

Ya nuna karara yadda ya cire kudade, sarkar wuya da shinfidar Sallah daga wasu abubuwan da ya aikata masu kama da siddabaru.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'

Wata Sabuwa: Mijin Aljanna Ya Bayyana Gasiyar Lamarinsa Auren Aljana
Wata Sabuwa: Mijin Aljanna Ya Bayyana Gasiyar Lamarinsa Auren Aljana Hoto: voahausa.com
Asali: UGC

Sai dai, a wani sabon bidiyo, Malam Kofar Na'isa ya karyata kansa da kansa, ya ce sam babu batun auren wata aljana, kuma yana haka ne don samun na kashewa daga hannun mutane, wanda ya ce hakan a yanzu ya faskara.

Da yake amsa tambayar mu'amalarsa da aljana, yace: "Ni abinda ya hada ni da aljana, na taso ne mahaifiyata tana da larurar aljanu shekara 42, to wannan mu'amalar ta da take shine yasa nima na shiga ciki."

Ya karyata mu'amalarsa da aljanu inda yake cewa: "Eh to, bangaren mu'amala da aljanu gaba da gaba, yi ne kawai don a karfafa masu sayen magani." Ya kara da cewa, "don na samu kudin kashewa dana abinci."

Kalli bidiyon hira da mijin aljana:

KU KARANTA: Sarkin Musulmi Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Soke Shirin NYSC

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Asabar ya tuna yadda wani gwamna ya shafa masa cutar COVID-19 shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito.

El-Rufai, yayin da yake jawabi a laccar Ahmadu Bello Foundation ta bakwai a Kaduna ranar Asabar, ya kuma ce akalla mutane 50,000 ne cutar za ta kashe a shekarar da ta gabata idan da ba a sanya takunkumi ba.

Gwamnan, a ranar 26 ga Maris, 2020, ya sanya takunkumi a jihar Kaduna, bayan barkewar cutar COVID-19 ya kuma dage dokar a ranar 9 ga Yunin, 2020, bayan kwanaki 75.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: