PDP ta dakatar da shugabanta saboda rashin da’a, ta sanar da madadinsa

PDP ta dakatar da shugabanta saboda rashin da’a, ta sanar da madadinsa

- Rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Edo ya ta'azzara bayan da jam'iyyar ta sanar da daukar matakan ladabtarwa ga daya daga cikin manyan mambobinta

- Reshen jam’iyyar ta bayyana wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugabanta na jihar Tony Aziegbemi, wanda a yanzu haka yake fuskantar bincike

- Shugaban da aka dakatar bai amsa tuhumar da ake yi masa ba tukuna amma an umarce shi da ya jira sakamakon bincike cikin ayyukansa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da shugabanta, a jihar Edo, Tony Aziegbemi bisa zargin aikata ba daidai ba, jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar jaridar The News, reshen Edo na jam'iyyar ta sanar da dakatarwar ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Chris Nehikhare, ya saki a ranar Laraba, 2 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Tawagar motocin ‘dan IBB sun yi hatsari, wasu sun rasa ransu

PDP ta dakatar da shugabanta saboda rashin da’a, ta sanar da madadinsa
PDP ta dakatar da shugabanta saboda rashin da’a, ta sanar da madadinsa
Asali: Twitter

Baya ga zargin aikata ba daidai ba, PDP ta kuma zargi Aziegbemi da haddasa tashin hankali da rashin hadin kai tsakanin mambobinta.

Jam’iyyar ta ce an yanke shawarar dakatar da shugaban ne a taron kwamitin aiki na jihar, da kashi biyu bisa uku na mambobinsa.

Reshen jam’iyyar na Edo ta bayyana cewa Harrison Omagbon, mataimakin shugaban jihar, zai yi aiki a madadinsa har sai an tabbatar da zargin da ake yi wa shugaban da aka dakatar.

Ta kuma bayyana cewa an kafa kwamitin bincike don bincikar zargin da ake yi wa shugaban tare da gabatar da rahoto ga kwamitin aiki na jam'iyyar a cikin mako guda.

KU KARANTA KUMA: Kyawawan tsoffin hotunan Shugaba Muhammadu Buhari 7 a matsayinsa na matashi da ke son iyalinsa da aiki

Jam'iyyar PDP ta Edo ta bukaci mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.

A wani lamarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yace ba shi da wani shiri na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a watan Yuni, 12.

Gwamnan yace bai yanke hukunci ko kuma ya tsayar da ranar komawa jam'iyyar APC ba.

A ranar Talata, jaridar Premium times ta ruwaito daga wata majiya dake kusa da gwamnan cewa, Gwamnan ya gama shirye-shiryen ficewa daga PDP a ranar 12 ga watan Yuni, a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da zaiyi a bikin ranar demokaraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel