'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi

'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi

- Sanata Aliyu Sabi Abdullahi mai wakiltar Niger ta Arewa ya ce yan bindigan da sojoji suka kora daga Zamfara da Katsina ne suka dawo Niger

- Ɗan majalisar ya koka kan yadda ƴan bindiga suka yi kaka gida a wasu kananan hukumomi biyar da ke ƙarƙashin mazabarsa

- Sanata Sabi Aliyu ya yi kira ga jami'an tsaro da sauran wadanda abin ya rataya a kansu su kai wa jihar Niger da sauran wurare ɗauki

Sanata mai wakiltar mazabar Niger ta Arewa, Aliyu Sabi Abdullahi ya ce yan bindigan da sojoji suka fatattaka daga jihohin Zamfara da Katsina ne suke dawowa jihar Niger.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tattauna batun a zauren Majalisar na tarayya a ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi
'Yan Bindigan Da Aka Fatattaka Daga Katsina Da Zamfara Ne Ke Addabar Ƴan Neja, Sanata Abdullahi. Hoto: @ChannelsTV
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

Dan majalisar ya ce ƴan bindigan suna yawan kai hare-hare a ƙananan hukumomi biyar da ke karkashin mazabarsa.

Ya ce tsakanin yammacin ranar Litinin da safiyar Talata, mutum takwas ne aka kashe yayin da dama sun jikkata a harin da aka kai wasu garuruwa kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a jihar Niger.

A cewarsa, hare-haren ya tilasta wa fiye da mutum 50,000 barin gidajen su suna neman ɗauki a sansanin ƴan gudun hijira wato IDP.

KU KARANTA: Sabon Salo: 'Yan fashi sun fara zuwa sata gidajen mutane da na'urar POS

Don haka, ya bukaci jami'an tsaro da wadanda abin ya shafa su ƙarasa jihar Niger da wasu jihohin da yan bindigan ke adabar mutane don murkushe su.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel