Rahoto: An Gargadi Ahmed Gulak Kada Ya Tafi Imo, Amma Ya Yi Biris
- Wani rahoto da ya fito yayi karin haske game da abubuwan da suka faru kafin Ahmed Gulak, jigon APC, ya gamu da ajalin sa a jihar Imo
- Kisan Gulak ya zama abin mamaki ga ‘yan Najeriya da dama kuma wasu masana harkokin tsaro sun yi tambayar dalilin da yasa dan siyasar ba shi da tsaro
- ‘Yan sanda sun zargi wata kungiyar 'yan aware a kudu maso gabas da kisan Gulak, amma gwamnan jihar Imo ya yi tirjiya game da ikirarin na ‘yan sanda
Wani rahoto na musamman da jaridar The Cable ta fitar ta yi ikirarin cewa an gargadi Ahmed Gulak, sanannen jigo a jam’iyyar APC kan yin tafiya zuwa jihar Imo inda daga karshe aka harbe shi.
Jaridar, ta ambato wata majiya, da ta bayyana cewa Gulak ya yanke shawarar zuwa Owerri, babban birnin jihar Imo, domin jin ra’ayoyin jama’a game da sake duba kundin tsarin mulki, duk da gargadin da aka yi masa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Shugaban INEC, Kwamishinoni
An ce marigayi dan siyasar ya dage kan tafiyarsa, yana mai cewa dukkanmu 'yan Najeriya ne.
Mai binciken ya ce:
“Babu wanda ya ke son a tura shi Owerri amma Gulak ya yanke shawarar zuwa. Da farko an so ya tafi Gombe amma ya yanke shawarar kin hakan lokacin da ya bayyana ba wanda yake da sha'awar zuwa Owerri.
"Mun tilasta masa kada ya tafi, amma ya jajirce wajen gudanar da aikin, duk da cewa masu ba da shawara daga yankin kudu maso gabas sun ki amincewa da aikin."
Wasu ‘yan bindiga sun harbe Gulak a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, yayin da yake komawa Abuja daga Owerri.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun harbe Gulak a yayin da yake komawa Abuja daga Owerri, babban birnin jihar Imo, a ranar Lahadi, TheCable ta ruwaito.
Da yake maida martani game da labarin, Jonathan ya yaba wa marigayin a matsayin "mai yi wa kasa hidima mai aminci", yana mai bayyana yadda yaji zafin mutuwarsa.
Asali: Legit.ng