El-Rufai Ya Sake Sabbin Nadi a Gwamnatinsa, Ya Yi Garambawul a Wasu Wurare
- Gwamnatin El-Rufai ta sake sabbin nadin sakatorin din-din-din har mutum biyar a wasu ma'aikatu
- Gwamnan ya bayyana sunayensu, tare da bayyana ma'aikatun da za su yi aiki a matsayin sakatarorin na din-din-din
- Hakazalika ya yabawa wasu jami'an da za su yi ritaya, yana mai cewa sun doge kan aiki tukuru a jihar
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi sabbin nadi a wasu ma'aikatun jihar, in da kuma aka sauyawa wasu da dama ma'aikatu.
A wata sanarwa da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa ya fitar wanda Legit.ng Hausa ta gano, gwamnan ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kaduna na sanar da nadin sabbin sakatarorin din-din-din a jihar.
KU KARANTA: Rahoto: An Gargadi Ahmed Gulak Kada Ya Tafi Imo, Amma Ya Yi Biris
Sanarwar ta ce: "KDSG ta nada sabbin Sakatarorin din-din-din guda biyar kuma ta sanar da sabbin turawa ga wadannan manyan jami'ai:
1.Abubakar Abba Umar
2.Yusuf Sale
3.Adamu A. Atama
4.Balarabe Wakili
5.Ya’u Y. Tanko."
Sanarwar ta kuma bayyana ma'aikatun da aka tura sakatarorin na din-din-din guda 21. Hakazalika gwamna El-Rufai ya yaba da aikin sakatarori uku na musamman; Musa Adamu, Amina Adamu Ikara da Sabiu Sani, wadanda za su yi ritaya daga aiki.
KU KARANTA: Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi
A wani labarin, Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun ba da rahoton wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Goska a karamar hukumar Jema’a da ke jihar ta Kaduna, inda suka kashe mutum hudu.
Samuel Aruwan, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, na Jihar Kaduna, ya fada a ranar Talata cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin suka kashe mutanen hudu.
“Wadanda aka kashen sunayensu; Wakili Kon, Yusuf Joshua, Martha Ayuba da Lami Peter," in ji shi.
Asali: Legit.ng