Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed

Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed

- Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, yace ayyukan cigaban da gwamnatin Buhari Tayi zasu amfanar da mutane da dama nan gaba

- Ministan yace ba a taɓa samun wata gwamnati ba da ta samu nasarori ba kaɗan ɗin da take samu kamar wannan gwamnatin

- Ministan ya faɗi haka ne a Abuja, yayin da yake jawabi ga manema labarai a wurin bikin cikar gwamnatin shekara 2 a zango na biyu

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace nasarorin da gwamnatin shugaban ƙasa Buhari ta cimma zai amfanar da mutanen zamani da dama masu zuwa, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Dumi-Ɗumi: Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Tabbatar da Nadin Sabon COAS, Manjo Janar Yahaya

Ministan ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed
Ba’a Taɓa Samun Gwamnati a Tarihin Najeriya da Tayi Ayyukan Cigaba Kamar Ta Buhari Ba, Lai Muhammed Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewarsa, ba'a taɓa yin wata gwamnati ba a tarihin Najeriya data samu nasarori masu ɗimbin yawa da ƙarancin kuɗin shiga kamar gwamnatin shugaba Buhari.

Ministan Yace:

"Ba'a taba samun wata gwamnati ba a tarihin Najeriya da tayi ayyuka masu ɗimbin yawa ba ƙaɗan ba kamar wannan gwamnatin."

"Abu ne mai sauki a manta, amma lokacin da gwamnatin nan ta shiga ofis a 2015, farashin ɗanyen man fetur da ƙasar ta dogara da shi kashi 95% ya faɗi warwas a kasuwar duniya."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Islamiyyar da Aka Sace Ɗalibanta a Neja Yayi Magana da Yan Bindiga Ta Wayar Tarho

"Hanyoyin mota da na jirgin ƙasa, gadar sama, samar da gidaje masu ɗimbin yawa, cigaban tashoshin ruwa, ƙarin samun hasken wutar lantarki da sauran ayyukan cigaba da Buhari yayi zasu amfana har ga mutanen da zasu zo nan gaba.

A wani labarin kuma Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr Isa Pantami, yace za'a samar da cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) akalla ɗaya a kowace jiha, kamar yadda Daily Nigerian ra ruwaito.

Ministan yace a halin yanzun ma'aikatarsa ta ƙaddamar da ECC 23 a faɗin ƙasar nan kuma akwai sauran 13 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel