'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna

- Hukumonin tsaro a jihar Kaduna sun tabbatar da hallaka wasu mutane a yankin jihar ta Kaduna

- Rahoton tsaro daga kwamishinan tsaron cikin gida ne ya tabbatar da kisan mutum hudu a jihar

- An kuma raunata wata mata, wacce aka yi gaggawan daukar ta zuwa asibiti don mata magani

Hukumomin tsaro a jihar Kaduna sun ba da rahoton wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Goska a karamar hukumar Jema’a da ke jihar ta Kaduna, inda suka kashe mutum hudu.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, na Jihar Kaduna, ya fada a ranar Talata cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin suka kashe mutanen hudu.

“Wadanda aka kashen sunayensu; Wakili Kon, Yusuf Joshua, Martha Ayuba da Lami Peter," in ji shi.

KU KARANTA: Akwai Matsala: Kungiyar Arewa Ta Gargadi 'Yan Arewa Kan Zuwa Yankin Kudanci

'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna
'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna Hoto: newscentral.africa
Asali: UGC

A cewar kwamishinan, “Maharan sun kai hari ne tare da kashe Wakili Kon da Yusuf Joshua a gonakinsu."

"Wata mata, Laraba Silas, ta samu rauni na harbin bindiga kuma an garzaya da ita asibiti."

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bakin ciki game da rahotannin tare da yin addu'ar Allah ya jikan rayukan mazaunan da 'yan bindigan suka kashe.

"Gwamnan ya aike da ta'aziya ga danginsu, tare da yi wa matar da aka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa."

"Jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da sintiri a yankin, tare da bincike kan harin."

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da lamurran tsaro suka tabarbare a yankin Arewacin Najeriya, inda ake yawan sace mutane da hallakasu.

Channels Tv ta ruwaito cewa, a karshen makon da ya gabata ne 'yan bindiga suka sako wasu daliban da aka sace na jami'ar Greenfield dake jihar ta Kaduna bayan shafe kwanaki sama da 30 a hannun 'yan bindigan.

KU KARANTA: Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Da Hukumar NECO Sun Magantu

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban makarantar sakandaren Gwamnati ta Ruma da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, Malam Sa’idu Usha.

Mazauna yankin sun ce an sace Usha ne da yammacin ranar Juma’a bayan an tashi daga makaranta a kan hanyarsa ta komawa Batsari daga Ruma, jaridar Punch ta rwauito.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun bar babur din da Usha ke kai suka shilla dashi cikin dajin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel