Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Shugaban INEC, Kwamishinoni

Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa Da Shugaban INEC, Kwamishinoni

- Shugaba Buhari ya gana da shugaban hukumar INEC biyo bayan hare-hare da ake kai wa ofisoshin hukumar

- A tare da shugaban na INEC akwai kwamishinoni biyar da aka yi tattaunawar dasu a Abuja

- Ana sa ran sun tattauana mafita ne kan karuwar hare-hare da ake kai wa ofishoshin INEC a fadin kasar

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gana da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, Channels Tv ta ruwaito.

Farfesa Yakubu ya kasance tare da kwamishinonin INEC guda biyar a taron, wanda aka yi a dakin taro na Uwargidan Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Taron na iya zama mai nasaba da hare-haren da aka kai kan cibiyoyin INEC na baya-bayan nan a duk fadin kasar.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Dira Kan Manoma, Sun Kashe 4, Sun Raunata Wata Mata a Kaduna

Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa dDa Shugaban INEC, Kwamishinoni
Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawar Gaggawa dDa Shugaban INEC, Kwamishinoni Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahoton Premium Times ya ruwaito shugabn na INEC a ranar 27 ga Mayu, yana cewa an kai wa ofisoshi da wuraren aikinta hari sau 41 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sai dai, a cikin makonni hudun da suka gabata, ofisoshin hukumar guda 11 ko dai an cinna musu wuta ko an lalata su, a cewar shugaban na INEC.

A ranar Litinin, hukumar zaben ta sha alwashin gudanar da zaben gwamnan Anambra, wanda aka shirya za a yi a ranar 6 ga Nuwamba, duk da karuwar matakan rashin tsaro a fadin kasar.

KU KARANTA: Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Da Hukumar NECO Sun Magantu

A wani labarin, Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta gargadi ‘yan Arewa kan tafiya zuwa yankin Kudu maso Gabas a yanzu saboda halin da ake ciki na rashin tsaro.

Ta ba da shawarar cewa idan tafiyar ta zama dole, to a yi amfani da jami'an tsaro a ciki, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Wannan ya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, ya fitar a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel