Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Da Hukumar NECO Sun Magantu

Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Da Hukumar NECO Sun Magantu

- Rundunar 'yan sanda tare jami'an NECO sun bayyana gaskiyar abinda ya faru da shugaban NECO

- Sun ce lallai ba kashe shi aka yi ba, kawai ya mutu ne a cikin gidansa na Minna saboda karar kwana

- 'Yan sanda da hukumar NECO sun bayyana rahoton da ke cewa an kashe shugaban na NECO da zunzurutun karya

A yau Talata ne aka wayi gari da labarin mutuwar shugaban hukumar jarrabawa ta NECO, wanda aka ce wasu ne suka kashe shi, jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai, majiyoyi masu karfi daga garin Minna a jihar Neja sun yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe Farfesa Godswill Obioma, shugaban na Hukumar Kula da Jarabawa ta Kasa (NECO).

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samo daga hukumar, NECO tace Obioma ya mutu ne kawai sabanin yadda aka ce wai an kashe shi.

KU KARANTA: Akwai Matsala: Kungiyar Arewa Ta Gargadi 'Yan Arewa Kan Zuwa Yankin Kudanci

Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Sun Magantu
Ba Kashe Shugaban Hukumar NECO Aka Yi Ba, 'Yan Sanda Sun Magantu Hoto: neco.gov.ng
Asali: UGC

A cewar wasu manyan jami’an NECO wadanda suka zanta da wakilin PM News, Obioma ya zo ne daga Abuja a safiyar Litinin, ba daren Litinin ba.

Jami’an NECO wadanda suka ziyarce shi da misalin karfe 9 na safe a gidansa da ke Dutsen Kura a Minna, Obioma ya fada musu cewa nan ba da dadewa ba zai fito zuwa ofishin na NECO.

Amma har zuwa karfe 2 na rana, Obioma bai bayyana ba, inda suka sake yin wata tawaga zuwa gidansa.

Wakilan sun same shi shi kadai a cikin babban dakin kwanansa, yana kwance, yana fuskantar kasa matacce, lamarin da yasa aka kira dan'uwansa, wanda yake zaune a Minna akan yazo ya ga gawar. Daga nan aka kwashi gawarsa zuwa Abuja.

Rundunar ‘yan sanda da jami’an NECO sun bayyana labarin kisan a matsayin labarin karya da kuma shaidar matarsa, Elizabeth.

An nada Obioma, mai shekara 67, a bara a watan Mayu a matsayin shugaban NECO, kuma asalinsa ya fito ne daga jihar Abia.

KU KARANTA: Wata Sabuwa: Mijin Aljana Ya Bayyana Gasiyar Lamarinsa Na Auren Aljana

A wani labarin daban, 'Yan sanda a babban birnin Tarayya Abuja sun harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon dan takarar shugaban kasa yayin wata zanga-zanga a bakin Unity Fountain dake a Abuja.

An harbiu Sowore a gefen dama a cinya lamarin da ya sa aka yi gaggawan wucewa dashi asibiti.

Ya rubuta a shafin Tuwita: "Yanzun nan 'yar sanda, ACP Atine ta harbe ni a Unity Fountain a Abuja. #RevolutionNow Yanzu aka fara gwagwarmaya za ta ci gaba koda kuwa za su dauki raina!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel