Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Islamiyyar da Aka Sace Ɗalibanta a Neja Yayi Magana da Yan Bindiga Ta Wayar Tarho
- Shugaban makarantar Islamiyyar da aka sace ɗalibanta a jihar Neja yace ya tattauna da yan bindigan
- A ranar Lahadi da ta gabata ne wasu yan bindiga suka kutsa cikin wata islamiyya a Tegina, inda suka sace ɗalibai da dama
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya baiwa jami'an tsaro umarnin ceto ɗaliban cikin gaggawa
Shugaban islamiyyar da yan bindiga suka sace ɗalibanta a jihar Neja ya samu zantawa da maharan.
KARANTA ANAN: Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike
Yan bindiga sun kutsa cikin makarantar Salihu Tanko Islamiyya dake garin Tegina, jihar Neja inda suka sace ɗalibai da dama, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
Abubakar Alhasan, shugaban makarantar ya faɗa wa BBC cewa ya yi magana da wasu daga cikin malamai da ɗaliban da aka sace.
Yace: "Mun gaisa da maharan na nemi alfarma a bar ɗaliban cikin koshin lafiya, kuma sun yi alƙawarin haka, amma sun ce ba zasu iya bayyana adadin ɗaliban dake hannun su ba."
"Malaman da na zanta da su sun ce ba a kashe kowa ba daga cikinsu kuma suna cikin koshin lafiya."
Shugaban islamiyyar yace duk da yan bindigan sunki bayyana adadin ɗaliban da suka sace amma hukumar makaranta ta gano yawansu
KARANTA ANAN: Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami
Yace: "bisa rahoton da muka samu daga iyayen yaran waɗanda suka faɗa mana basu ga 'yayan su ba, mungano cewan sun sace kimanin ɗalibai 136 a harin."
Malamin ya kuma bayyana cewa malamai guda uku ne a hannun yan bindigan saɓanin bakwai da ake yaɗawa.
Shugaban makarantar yace akwai ƴaƴan sa biyu a cikin ɗaliban da harin ya rutsa dasu.
A halin yanzu, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci jami'an tsaron ƙasar da su yi duk me yuwuwa su tabbatar sun kuɓutar da ɗaliban cikin gaggawa.
A wani labarin kuma Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah
Saudiyya ta yi martani kan wasu mutane dake sukar matakin data ɗauka na rage ƙarar lasifiƙun masallatai yayin kiran sallah.
A makon da ya gabata ne ƙasar ta baiwa masallatai umarnin rage ƙarar lasifiƙunsu zuwa mataki na ɗaya na ƙararsu.
Asali: Legit.ng