Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike

Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike

- Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya dakatad da Sarki da hakimi bisa zarginsu da hannu a ayyukan yan bindiga

- Waɗanda aka dakatad ɗin sune, Sarkin Ɗansadau, Hussaini Umar, da hakimin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala.

- Gwamnan ya naɗa kwamiti na musamman da ya ƙunshi amintattun mutane domin gudanar da bincike

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya dakatad da Sarkin Ɗansadau, Hussaini Umar, da hakimin Nasarawa Mailayi, Bello Wakkala, bisa zarginsu da hannu a ayyukan yan bindiga, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah

A cewar jawabin da mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai, Zailani Baffa, ya fitar yace dakatarwar zata fara aiki nan take, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa Gwamnan ya kuma umarci hakimin Ɗansadau ya cigaba da lura da al'amuran masarautar.

Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike
Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

Wani sashin jawabin yace: "An dakatad da hakimin Nasarawa Mailayi, Alhaji Bello Wakkala, kuma matakin dakatarwan zai fara aiki nan take."

Gwamnan ya amince da naɗa kwamitin amintattu da zasu gudanar da bincike tare da sa ido a kan sarakunan biyu da aka dakatar.

KARANTA ANAN: Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Yan kwamitin sun haɗa da; DIG Moh’d Ibrahim Tsafe a matsayin shugaba da kuma Barr. Abdurrasheed Haruna a matsayin sakatare.

Mambobin kwamitin sune: Hon. Yusuf Alhassan Kanoma, Hon. Ibrahim T Tukur, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, Sheikh Abdullahi Umar Dalla-Dalla, da kuma Sheikh Kabir Umar Maru.

Gwamnan ya umarci jami'an tsaro dasu zartar da harbi ga duk wani ɗan bindiga, ko wani mutum da suka gani ɗauke da bindiga in banda waɗanda doka ta amince su mallaki bindiga.

A wani labarin kuma Gwamnan Zamfara ya sallami dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sauke dukkan kwamishinoninsa da masu mukaman siyasa a jihar.

Gwamnan ya bukaci shugabannin hukumomi, ma'aikatu tare da duk mambobinsu da su mika ragamar mulkinsu ga manyan sakatarorinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel