Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mambobin IPOB Shida a Ebonyi, Ta Kwato Makamai a Hannun Su

Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mambobin IPOB Shida a Ebonyi, Ta Kwato Makamai a Hannun Su

- Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta cafke wasu da take zargin yan IPOB ne guda 6 tare da kwato makamai a hannun su

- Rundunar tace ta samu wannan nasara ne a wani Operation da jami'anta suka fita ranar Litinin

- Daga cikin makaman da suka kwato akwai, ƙananan bindigun Fistol guda biyar da kuma alburusai 12

Rundunar yan sanda a jihar Ebonyi ta cafke mutum 6 da take zargin mambobin ƙungiyan yan taware IPOB ne, kuma ta kwato makamai a hannun su, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Islamiyyar da Aka Sace Ɗalibanta a Neja Yayi Magana da Yan Bindiga Ta Wayar Tarho

Rundunar ta kwato makamai da suka haɗa da; Ƙananan bindigun fistol guda biyar, da kuma alburusai 12 daga hannun su.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, itace ta bayyana haka ranar Talata.

Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mambobin IPOB Shida a Ebonyi, Ta Kwato Makamai a Hannun Su
Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mambobin IPOB Shida a Ebonyi, Ta Kwato Makamai a Hannun Su Hoto: news24.com
Asali: UGC

Odah tace an kama waɗanda ake zargin ne a wani Operation da jami'ai suka fita ranar Monday domin watsa yan bindigan dake tilasta dokar zama a gida da IPOB ta saka.

Kakakin yan sandan ta kuma bayyana cewa jami'ai sun kashe wasu mutum uku da ake zargin yan fashi da makami ne, sun ƙwato wuƙaƙe, adduna da sauran makamai a hannun su.

KARANTA ANAN: Gwamna Matawalle Ya Dakatar da Sarki, Hakimi Bisa Zargin Taimaka Wa Yan Bindiga, Ya Naɗa Kwamitin Bincike

Ta bayyana cewa: "Bayan samun kiran gaggawa cewa wasu yan bindiga sun kai hari kan hanyar Ogbaga, suna cinna wa motoci wuta. Nan take aka tura jami'ai yankin."

"Yan ta'addan na ganin jami'an yan sanda sai suka buɗe musu wuta, suma suka maida martani. A wannan fafatawar ne biyu daga cikin maharan suka ji mummunan rauni, sauran suka tsere da harbin bindiga a jikinsu."

"Maharan sun ƙona wata motar Toyota Picnic, da sauran wasu motoci 5 a wurare daban-daban."

Odah ta kara da cewa sun kaiwa mazauna jihar hari ne sabida kawai sun fito, sunƙi bin dokar zama a gida da ƙungiyar IPOB ta sanya.

A wani labarin kuma Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr Isa Pantami, yace za'a samar da cibiyar amsa kiran gaggawa (ECC) akalla ɗaya a kowace jiha, kamar yadda daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan yace a halin yanzun ma'aikatarsa ta ƙaddamar da ECC 23 a faɗin ƙasar nan kuma akwai sauran 13 dake tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262