Sarkin Musulmi Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Soke Shirin NYSC

Sarkin Musulmi Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Soke Shirin NYSC

- Sarkin Musulmi ya bayyana ra'ayinsa game da yunkurin majalisar wakilai kan soke NYSC

- Ya ce duk masu fafutukar a soke NYSC ba sa nufin Najeriya da alheri duba da muhimmancin shirin

- A cewarsa, NYSC shiri ne da ya kamata a inganta ba wai a yi kokarin soke shi kwata-kwata ba

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, ya ce wadanda ke neman a soke shirin yiwa kasa hidimi na NYSC ba sa nufin Najeriya da alheri.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin wasu zababbun mambobin NYSC na rukunin 'A' diba na 2 da aka tura jihar Sokoto a fadarsa da ke Sokoto, Daily Trust ta ruwaito.

Maganar ta sarkin Musulmi martani ne ga yunkurin majalisar wakilai na soke shirin NYSC kwata-kwata a kasar duba da wasu dalilai da suka bayyana, jaridar Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'

Sarkin Musulmi Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Soke Shirin NYSC
Sarkin Musulmi Ya Yi Tsokaci Kan Yunkurin Soke Shirin NYSC Hoto: dailypost.ng
Asali: Depositphotos

Ya ce an kafa shirin na NYSC ne domin bunkasa hadin kan al’ummar kasar da kuma karfafa dankon zumunci a tsakanin ‘yan Najeriya.

Ya ce "Na ji ana kokarin soke shirin NYSC, ina baku tabbacin cewa wadanda ke bayan wannan gwagwarmaya ba sa nufin kasar nan da alheri," in ji shi.

A cewarsa, shirin na NYSC shine shirin da ake matukar bukata duba da halin da ake ciki a yanzu lokacin da aka kusan raba Najeriya ta hanyar nuna banbanci tsakanin kabilu da addinai.

Ya yi maraba da mambobin kungiyar bautar da aka tura jihar, yana mai cewa jihar ce mafi zaman lafiya a Najeriya.

Abubakar ya bukaci matasa masu yi wa kasa hidiman su dauki jihar a matsayin gidansu na biyu tare da lalubo damar da ke ciki domin su dama.

Ya shawarce su da su mutunta al'adu da zamantakewar al'ummomin da suka karbi bakuncinsu kuma su kula da tsaro saboda akwai kalubalen tsaro a sassan jihar.

KU KARANTA: Garba Shehu Ya Yabawa Gwamna Ganduje, Ya Gamsu Da Ci Gaban Da Kano Ta Samu

A wani labarin, Wata kungiyar farar hula, Center for Social Justice, Equity and Transparency (CESJET), ta yi Allah wadai da bijiro da wani kudiri na soke aikin bautar kasa na NYSC, da wani dan majalisar wakilai ya yi.

CESJET ta ce dokar da ke ba da shawarar dakatar da NYSC wani mummunan shiri ne ga matasan Najeriya. Kungiyar ta ce tunanin soke NYSC, ya samu goyon baya ne daga wakilai masu son hargitsa Najeriya.

Da yake magana a wani taron manema labarai wanda wakilin jaridar Legit.ng ya halarta a Abuja a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, babban sakataren CESJET, Isaac Ikpa, ya ce ba za a iya kwatanta muhimmancin shirin ga Najeriya ta yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel