Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'

Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'

- Hukumar jarrabawar shiga jami'a ta JAMB ta sanar da sabuwar ka'ida kan jarrabawar gwaji ta Mock

- Hukumar JAMB ta ce dole ne dukkan mai zana jarrabawar Mock ya biya N700 a cibiyar jarrabawa

- Hakazalika hukumar ta bayyana cewa, za a fara jarrabawar ne a ranar 3 ga watan Yuni mai zuwa

Hukumar jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta sanar da daliban da za su rubuta jarrabawar cewa dole ne su biya kudin rubuta jarrabawar gwaji wato 'mock' a cibiyoyin rubuta jarrabawa.

Sanarwar da JAMB ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce:

"Ana sanar da wadanda za su zana jarabawar 2021 Mock da aka shirya ranar Alhamis, 3 ga Yuni 2021 su je cibiyoyin da aka ba su tare da N700. Za su biya kudin ga mai Cibiyar azaman kudin jarrabawar mock."

KU KARANTA: Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje

Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock'
Da Dumi-Dumi: Dole Masu Rubuta Jarrabawar JAMB Su Biya N700 Kudin 'Mock' Hoto: technext.ng
Asali: UGC

Karin bayani nan kusa...

Asali: Legit.ng

Online view pixel