An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja

An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja

- Kungiyar hatsabibin dan bindiga, Na-Sanda ne suka kwashe daliban Islamiyya na Tegina dake jihar Neja

- Kungiyar Na-Sanda ce ta kwashe 'yam matan makarantar sakandare dake Jangebe a jihar Zamfara

- An gano cewa, mambobin kungiyar tare da iyalansu sun tattara komatsansu daga Zamfara zuwa Neja

Kungiyar 'yan bindiga da suka shirya sace 'yan matan makarantar sakandare ta Jangebe dake jihar Zamfara a farkon shekarar nan, sune ke da alhakin kwashe daliban Islamiyya a Tegina dake karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, Daily Trust ta tabbatar.

Mambobin kungiyar sun kwashe dalibai masu yawa daga jihar Neja a ranar Asabar da ta gabata, wata majiya mai karfi ta tsaro ta sanar da Daily Trust, duk da babu dalilin wannan aika-aikar har yanzu.

KU KARANTA: Lalacewar darajar Naira: Naira tana halin da yafi dacewa da ita, Garba Shehu

An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja
An gano hatsabibiyar kungiyar 'yan bindigan da suka sace yaran Islamiyya a Neja. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5

Gagararriyar kungiyar 'yan bindigan da ta samu jagorancin Na-Sanda, sun dade suna ta'asa a dajin Jangebe dake karamar hukumarr Talatan Mafara ta jihar Zamfara.

Na-Sanda kanshi dan asalin karamar hukumar Zurmi ne dake jihar Zamfaran.

'Yan bindiga daga kungiyar sun tsinkayi farfajiyar makarantar 'yammata a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 26 ga watan Fabrairu inda suka yi awon gaba da 'yammata kusan 300 daga dakunan baccinsu.

An sako 'yammatan bayan kwanaki hudu da sacesu, duk da kuwa ba a san ko an biya kudin fansa ba.

"Sun bar wurin tare da iyalansu a kan daruruwan babura," majiyar da ta bukaci a boye sunanta tace. Ta kara da cewa kungiyar na da mambobi kusan 500 kuma suna yawo kan babura sama da 300.

Bayan kamar mako daya da suka baro Zamfara zuwa jihar Neja, 'yan bindigan sun kai hari garin Tegina inda suka sace dalibai da malaman Islamiyyar Salihu Tanko dake garin.

Sun hada da jama'an da ba a san yawansu ba bayan kwashe yaran Islamiyyar, har da tsohon kansilan garin.

Har yanzu ba a san inda suka kai wadanda suka sace ba. Akwai dai rahotannin dake nuna cewa 'yan bindigan sun sako yara 11 wadanda suka kasa jure tafiyar kasan.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai mummunan hari garin Beri dake yankin Bobi na jihar Neja inda suka kona ofishin 'yan sanda tare da sheke sama da mutane 13 da suka hada da jami'in dan sanda.

Hukumar NEMA ce ta tabbatar da harin a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin wacce ta zo kasa da sa'o'i 24 da garkuwa da yaran Islamiyya a jihar.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, hukumar taimakon gaggawan tace wannan harin ya bar wasu jama'a da miyagun raunika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel