'Yan bindiga sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke mutum 13 a jihar Neja
- 'Yan bindiga sun kone ofishin 'yan sandan garin Beri a jihar Neja, sun halaka rayuka 13
- Hukumar NEMA ta tabbatar da aukuwar harin inda tace jami'in dan sanda 1 ya rasu
- An sake da tabbatar da cewa wasu mazauna yankin sun tsira da miyagun raunika
'Yan bindiga sun kai mummunan hari garin Beri dake yankin Bobi na jihar Neja inda suka kona ofishin 'yan sanda tare da sheke sama da mutane 13 da suka hada da jami'in dan sanda.
Hukumar NEMA ce ta tabbatar da harin a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin wacce ta zo kasa da sa'o'i 24 da garkuwa da yaran Islamiyya a jihar.
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, hukumar taimakon gaggawan tace wannan harin ya bar wasu jama'a da miyagun raunika.
'Yan bindigan sun kara da kai hari Unguwan Malam Bako dake yankin Kotonkoro kuma sun sace mutanen da har yanzu ba a san yawansu ba.
KU KARANTA: Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun saka hedkwatar jami'an hukumar shige da fice bam a Abia
Hukumar ta lissafo sunan mamatan kamar haka: Idris Ahmed Kwata, Hadiza Umaru Tunga, Momi Dalladi, Ibrahim Dalkadi, Yau Dalladi, Saadiya Garba, Garba Umar Tashanjirgi, Hussaini Shuaib, Ayuba Garba, Abdullahi Jodi, Alhaji Isah Kasakohi da Fatima Nasiru Kwata.
Jihar Neja ta fi kowacce jiha girma a kasar nan kuma tana daga cikin jihohin da miyagun al'amuran 'yan bindiga suka fi kamari a kasar nan.
A wata takarda da gwamnan jihar, Abubakar Bello, ya fitar a ranar Lahadi, ya kwatanta halin tsaron da jihar ke ciki da na yaki.
"Halin da ake ciki yanzu ya kai na rikici, a takaice zamu iya cewa yaki ne dole mu tunkare shi babu tsayawa," yace.
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa da fushinsa a kan abinda ya kira da "mummunan kisan gillan dan siyasar Adamawa Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo, wanda wasu 'yan bindiga suka yi."
A yayin martani ga aukuwar lamarin a ranar Lahadi, shugaban yace: "Na matukar fusata da kisan gillar da miyagun mutanen da basu son zaman lafiya, hadin kai da kuma cigaban kasar nan suka yi wa Gulak.
"Bari in ja kunne, babu wani mutum ko kungiya da zata yi irin abun nan ta tafi ba tare da fuskantar hukunci ba. Za mu yi amfani da dukkan karfinmu wurin tabbatar da cewa wannan mummunan al'amari da miyagun mutane basu sha ba."
Asali: Legit.ng