Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5

Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5

- Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoni 4 da hadimansa 5 bayan komawa APC

- Duk da gwamnan bai sanar da dalilinsa na yin hakan ba, ya mika godiyarsa ga tsoffin kwamishinonin da hadiman

- Kwamishinonin da ya sallama sun hada da na lamurran mata, habaka sabon birni, yada labarai da sauransu

Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya sallami kwamishinoninsa hudu bayan sauya sheka da yayi daga jam'iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki kasa da makonni biyu.

Mai baiwa gwamnan shawara ta musamman a fannin yada labarai, Christian Ita, ta sanar a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin a garin Calabar, babban birnin jihar, Daily Nigerian ta tabbatar.

Kamar yadda takardar tace, kwamishinonin da lamarin ya shafa sun hada da Mike Usibe (Kwamishinan sabon birni), Rita Ayim (Kwamishinan harkokin mata), Asu Okang (Kwamishinan yada labarai) da Ntufam Etim (Kwamishinan sauyin yanayi).

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan tsuleliyar budurwa 'yar Najeriya da ta fara tuka jirgin sama a shekaru 17

Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5
Bayan kwanaki da barin APC, Ayade ya sallami kwamishinoni 4 da hadimai 5. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mansurah Isah ta sanar da rabuwar aurensu da Jarumi Sani Danja

Ayade ya kara da sauwakewa hadimansa biyar mukaminsu. Hadiman sun hada da: Leo Inyambe, Orok Duke, Victor Okon, John Bassey, da Mbeh Agbiji.

Kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito, duk da gwamnan bai bada dalilinsa na sallamarsu ba, ya mika godiyarsa ga kwamishinonin da hadiman kan ayyukan da suka yi wa jihar kuma yayi musu fatan alheri.

Legit.ng ta ruwaito yadda Ayade ya sanar da hukuncinsa a ranar Alhamis, 20 ga watan Mayu a wani taro da yayi da gwamnonin APC shida wadanda suka kai masa ziyara har gidan gwamnatinsa.

A wani labari na daban, 'yan bindiga wadanda ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne sun kai mugun hari hedkwatar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya dake Ubakala, karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Anambra.

Hedkwatar hukumar bata da tazara da inda 'yan sanda suke wadanda aka kaiwa hari tun farko a Ubakala kuma hakan ya kawo mutuwar jami'an 'yan sandan biyu, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa sun sakawa hukumar NIS bam inda ya tashi da ita sannan suka budewa jami'an dake aiki wuta, lamarin da ya kawo ajalin wasu daga ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng