Lalacewar darajar Naira: Naira tana halin da yafi dacewa da ita, Garba Shehu

Lalacewar darajar Naira: Naira tana halin da yafi dacewa da ita, Garba Shehu

- Malam Garba shehu, mai magana da yawun shugaban kasa yace naira tana darajar da yafi dacewa da ita a halin yanzu

- Shehu yace idan aka yi duba da annobar korona, Najeriya ce kasa daya tak a Afrika dake samun habakar tattalin arziki

- Ya tabbatar da cewa shugaban kasa na aiki babu dare, babu rana domin ganin 'yan Najeriya basu kwana da yunwa ba

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, yace naira tana halin da yafi dacewa da ita duba da halin da muke ciki.

A ranar Alhamis da ta gabata, naira ta kara daraja da kashi 0.1 inda ta koma N411 daidai da $1 amma kuma ta rage daraja da kashi 0.4 a kasuwar tsaye inda ta koma N495 daidai da $1.

A yayin jawabi a shirin siyasa na ranar Lahadi da gidan talabijin na Channels, Shehu yace kusan shekara daya da ta gabata, annobar korona ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

KU KARANTA: Bidiyon sojoji sun kacame da murna bayan an sanar da Farouk Yahaya matsayin COAS

Lalacewar darajar Naira: Naira tana halin da yafi dacewa da ita, Garba Shehu
Lalacewar darajar Naira: Naira tana halin da yafi dacewa da ita, Garba Shehu. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo da hotunan tsuleliyar budurwa 'yar Najeriya da ta fara tuka jirgin sama a shekaru 17

Mai magana da yawun shugaban kasan yayi ikirarin cewa tattalin arzikin Najeriya ne kadai a Afrika yake ta habaka.

Shehu ya yi wannan tsokacin ne bayan gabatar masa da kiyasin yadda tattalin arzikin kasar nan ke tafiya tun daga 2015 zuwa 2021.

A martaninsa, yace ministan kudi ce take da hurumin yin tsokaci kan tattalin arzikin kasa.

A yayin da aka tambayeshi akan kalubalen da dokokin tattalin arzikin na gwamnati ke fuskanta, yace duk mai kalubalantar yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da tattalin arzikin kasar nan "ya je a duba shi".

"Idan ka yi min wannan tambayar, zan ce duk wanda yake kalubalantar yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arzikin kasar nan na bukatar a sake duba shi," yace.

"Ka duba duk abubuwan da suka faru saboda annobar korona a shekarar da ta gabata. Zaku ga cewa a dukkan nahiyar Afrika, wannan kasar ce kadai ke ganin daidai a fannin habakar tattalin arziki."

Shehu yace gwamnatin Buhari na aiki babu dare, babu rana wurin tabbatar da cewa 'yan Najeriya basu kwana da yunwa ba.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa da fushinsa a kan abinda ya kira da "mummunan kisan gillan dan siyasar Adamawa Ahmed Gulak a Owerri, jihar Imo, wanda wasu 'yan bindiga suka yi."

A yayin martani ga aukuwar lamarin a ranar Lahadi, shugaban yace: "Na matukar fusata da kisan gillar da miyagun mutanen da basu son zaman lafiya, hadin kai da kuma cigaban kasar nan suka yi wa Gulak.

"Bari in ja kunne, babu wani mutum ko kungiya da zata yi irin abun nan ta tafi ba tare da fuskantar hukunci ba. Za mu yi amfani da dukkan karfinmu wurin tabbatar da cewa wannan mummunan al'amari da miyagun mutane basu sha ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel