Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah

Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah

- Saudiyya ta yi martani kan wasu mutane dake sukar matakin data ɗauka na rage ƙarar lasifiƙun masallatai yayin kiran sallah

- A makon da ya gabata ne ƙasar ta baiwa masallatai umarnin rage ƙarar lasifiƙunsu zuwa mataki na ɗaya na ƙararsu

- Ma'aikatar harkokin addinin musulunci tace masu sukar matakin makiya ne dake son tada husuma

Ƙasar Saudi Arabia ta maida martani kan mutanen dake sukar matakin da ta ɗauka na rage ƙarar kiran sallah a masallatai.

KARANTA ANAN: Gwamna Zulum Ya Sake Kulle Sansanin Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa Saudiyya ta bada umarni ga masallatai su rage ƙarar lasifikokin su yayin kiran sallah.

Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah
Saudiyya Ta Maida Martani Kan Masu Sukar Matakinta Na Rage Ƙarar Kiran Sallah Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Rahoton BBC ya nuna cewa ma'aikatar harkokin addinin musulunci ta ƙasar ta maida martani kan wasu mutane dake sukar matakin.

Abdul-lateef Sheikh ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama'a ke yi kan ƙarar kiran sallah.

KARANTA ANAN: Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Daga cikin waɗanda suka yi ƙorafin kan ƙarar ƙiran sallah, akwai iyaye waɗanda suka bayad da dalilin su cewa ƙarar lasifikun masallatai na hana 'ya'yansu barci.

A makon da ya gabata ne, ma'aikatar ta umarci masallatai a ƙasar su rage ƙarar na'urar kiran sallah zuwa kashi ɗaya na ƙararta.

Al-Sheikh yace: "Masu sukar wannan matakin maƙiya ne kuma masu son tada husuma a tsakanin jama'a."

A wani labarin kuma Hameed Ali Ya Kafa Sabon Tarihi, Ƴa Samar da Biliyan N799bn Cikin Watanni 5 kacal

Hukumar kwastam ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Hameed Ali ta kafa sabon tarihi na samar da kuɗin shiga ga gwamnati.

A karo na farko NCS ta samar da kuɗaɗen shiga kimanin biliyan N799bn a cikin watanni biyar kacal, kamr yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel