Gwamna Zulum Ya Sake Kulle Sansanin Yan Gudun Hijira a Maiduguri

Gwamna Zulum Ya Sake Kulle Sansanin Yan Gudun Hijira a Maiduguri

- Gwamnatin jihar Borno ta sake kulle wani sansanin yan gudun hijira dake Maiduguri, babban birnin jihar

- Gwamnatin tace ta kammala shirin kulle dukan sansanonin dake faɗin jihar kafin ƙarshen wannan shekarar

- Wannan dai duk yana cikin shirin gwamnatin Borno na maida yan gudun hijira zuwa gidajen su na asali

Gwamnatin jihar Borno ta sake kulle sansanin yan gudun hijira (IDP) dake sansanin bada horo na NYSC a Maiduguri, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Zuwa 2022, Kowace Jiha a Najeriya Zata Sami Cibiyar Amsa Kiran Gaggawa, Sheikh Pantami

Legit.ng ta gano cewa wasu jami'an gwamnatin jihar Borno ne suka jagoranci kulle sansanin, wanda ke ɗauke da gidaje 1,464.

Sansanin shine na biyu da gwamnatin ta kulle cikin kwanaki uku a shirinta na maida mutanen dake wajen zuwa garuruwansu.

Gwamna Zulum Ya Sake Kulle Sansanin Yan Gudun Hijira a Maiduguri
Gwamna Zulum Ya Sake Kulle Sansanin Yan Gudun Hijira a Maiduguri Hoto: @Profzulum
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wurin kulle sansanin, Mustafa Gubio, kwamishinan sake gini da gyaran gine-gine, yace an kulle sansanin ne don a sami damar gudanar da aikin gyaran wurin.

Da yake nasa jawabin, kwamishinan aikin gona, Bukar Talba, yace gwamnatin jihar ta samar da gonaki a garin Auno da Damasak waɗanda zata baiwa mutanen da aka maida gidajen su yayin da damuna ke ƙaratowa.

Mr. Talba ya ƙara da cewa an kammala shirya jami'an tsaron NSCDC domin su bada tsaro ga manoma da gonaki a yankin.

KARANTA ANAN: NCS: Hameed Ali Ya Kafa Sabon Tarihi, Ƴa Samar da Biliyan N799bn Cikin Watanni 5

Hakanan kuma, daraktan hukumar bada agajin gaggawa (NEMA), Yabawa Kolo, yace gwamnati tayi tsarin kulle dukkan sansanin yan gudun hijiran dake jihar zuwa Disamba 2021.

Yace: "Gwamnati zata sake kulle sansanin dake Monguno mako mai zuwa domin maida mutanen gidajensu. Gwamnatin tayi shirin kammala kulle dukka sansanonin dake jihar zuwa Disamba 2021."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kutsa Jami'ar Jihar Taraba, Sun Yi Awon Gaba da Malami

Wasu yan bindiga sun kutsa kai gidajen kwanan malaman jami'ar jihar Taraba , inda suka sace wani lakcara, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Shugaban Makarantar (VC), Farfesa Ado-Tenebe ya tabbatar da faruwar lamarin, yace yayi matuƙar mamaki yadda akai haka ta faru a jami'arsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel