Ba Zaku Tsira Ba, Sai Na Hukunta Ku: Buhari Ga Wadanda Suka Kashe Ahmed Gulak

Ba Zaku Tsira Ba, Sai Na Hukunta Ku: Buhari Ga Wadanda Suka Kashe Ahmed Gulak

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin dadinsa bisa kashe Ahmed Gulak

- Ya ce wadanda suka aikata aikin dole ne a zakulo su domin a tabbatar an hukunta su a dokance

- Hakazalika ya tura sakon ta'aziyya da jaje ga iyalai, abokai da 'yan uwan marigayi Ahmed Gulak

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce wadanda ke da alhakin mutuwar dan siyasar Adamawa, Ahmed Gulak, ba za su tafi ba tare da an hukunta su ba.

An kashe Gulak a jihar Imo yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a ranar Lahadi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce lallai ya girgiza kuma ya kyamaci abinda aka aikatawa marigayin.

KU KARANTA: Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

Ba Zaku Tsira Ba, Sai Na Hukunta Ku: Buhari Ga Wadanda Suka Kashe Ahmed Gulak
Ba Zaku Tsira Ba, Sai Na Hukunta Ku: Buhari Ga Wadanda Suka Kashe Ahmed Gulak Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Shugaban ya ce: “Na yi Allah wadai da irin wannan mummunan shiri na kisan Gulak da mugayen mutane da suka kuduri aniyar lalata zaman lafiya, hadin kai da kuma cikakken yankin kasarmu suka yi.

“Bari in yi kashedi cewa babu wani ko wasu gungun mutanen da suka aikata wannan munanan aiki da za su tsira.

"Za mu yi amfani da duk karfin da muke da shi wajen tabbatar da cewa an gurfanar da irin wadannan baragurbi da muggan a gaban kotu.”

Shugaba Buhari ya jajantawa dangin mamacin, mutane da gwamnatin jihar Adamawa gami da abokansa a duk fadin kasar.

KU KARANTA: Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba

A wani labarin, Kungiyar mutanen Biafra ta IPOB ta ce “ba ta san komai ba” game da mutuwar Ahmed Gulak, wani jigo a jam’iyyar APC wanda aka kashe a jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Kungiyar a cikin wata sanarwa ta ce zarginta da kisan Gulak daidai yake da aibanta ta lokacin da "'yan ta'adda sanye da kayan jami'an tsaro ke aikata munanan abubuwa a Kudu maso Gabas."

An ruwaito yadda aka kashe Gulak, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Lahadi a Owerri, babban birnin jihar Imo, yayin da ya dawo Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel