Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

Biyo bayan bindige tsohon hadimin Jonathan, Ahmed Gulak a jihar Imo, jama'a da dama sun bayyana yanayin da suka ji game da mutuwarsa.

A yau aka samu rahoton cewa an kashe tsohon hadimin a cikin motarsa kuma kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sharhin jama'a 'yan Najeriya game mutuwar Ahmad Gulak, musamman daga kafar Tuwita.

KU KARANTA: Mun Biya Fansan N180000000 Kafin a Sako 'Ya'yanmu, Iyayen Daliban Greenfield

Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak
Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak Hoto: punchng.com

@ShehuSani ya rubuta a Tuwita cewa:

"Ahmed Gulak da aka kashe a Imo da dan majalisa mai wakiltar Kaduna daga Akwanga da aka sace; Hanyoyin tafiye-tafiye a mota a wasu sassan kasar sun zama masu hatsari da kuma bala'i."

@ogundamisi kuwa cewa ya yi:

"Muguwar kungiyar nan da ake kira "Liberation group" wacce ke ci gaba da samun yabo daga wurin jama'ar gari wadanda aka fi sani da kuma 'Yan Bindigan da Ba a Sansu ba' 'sun kashe Ahmed Gulak a Owerri Jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya."

@realFFK ya ce:

"Ina Allah wadai da kisan da aka yiwa tsohon abokina kuma tsohon Mataimaki na musamman ga @GEJonathan, Ahmed Gulak, a Owerri da safiyar yau. Matsorata sun bi shi, sun yi masa dirar mikiya, sun gano shi kuma sun kashe shi. Wannan aikin kwararrun 'yan ta'adda ne. Da fatan Allah ya jikan Ahmad."

@renoomokri ya jajantawa iyalansa tare da bayyana waye Ahmad Gulak, inda yake cewa:

"Mutuwar Ahmed Gulak ta yi min zafi. Komai yaya yanayin mutuwarsa take, ba zai kawo wa Najeriya alheri ba. Yana da tunanin da baya raina mutane saboda qabila ko addini. Ana bukatar irin wadannan mutane. Ina jajantawa danginsa. Da fatan Allah Ya ba su hakurin jure rashin."

@amasonic kuwa kalubalantar masu tambayar me ya kai Gulak Owerri ya yi. Ya ce:

"Wadanda ke tambayar abin da Ahmed Gulak yaje yi a Owerri inda aka kashe shi - Ina bukatar in fahimci ma'anar wannan tambayar. Bai kamata ya je wurin ba ne ko Owerri ba ta da aminci ga kowa da zai je cikinta?"

@obi_Nwosu ya ce:

"Ina jajantawa dangin marigayi Ahmed Gulak da aka kashe a Owerri jiya. Hotuna daga wurin da abin ya faru sun nuna cewa wannan na iya zama dalilin siyasa. Ya kamata ‘yan sanda su gudanar da cikakken bincike, ba kawai nuna yatsu ga IPOB ko ESN ba."

KU KARANTA: Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina

A wani labarin, A yau 30 ga watan Mayu aka harbe fitaccen dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Ahmed Gulak a Owerri, babban birnin jihar Imo, akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Sam Mbakwe na Kasa da Kasa.

Mutuwar Gulak ta zo ne yayin da ake fama da karuwar rashin tsaro a kudu maso gabas da kudu maso kudu, tare da majiyoyi da suka tabbatar da cewa an kai masa harin ne a cikin motarsa ​​ta Camry mai lamba Texas BFT 2150.

Labarin mutuwarsa ya bayyana ne daga abokin karatunsa, Dakta Umar Ado a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel