Kungiyar 'Yan Tawaye Ta IPOB Ta Yi Martani Kan Zarginta Da Kashe Ahmed Gulak

Kungiyar 'Yan Tawaye Ta IPOB Ta Yi Martani Kan Zarginta Da Kashe Ahmed Gulak

- Biyo bayan kashe Ahmed Gulak, an yi ta zargin kungiyar mutanen Biafra da aikata laifin

- Sai dai kungiyar ta musanta laifin tare da bayyana matsayar ta game da kashe 'yan siyasa

- Ta kuma yi ishara ga wadanda ya kamata a bincika ba wai ita ba a matsayinta na kungiya

Kungiyar mutanen Biafra ta IPOB ta ce “ba ta san komai ba” game da mutuwar Ahmed Gulak, wani jigo a jam’iyyar APC wanda aka kashe a jihar Imo, TheCable ta ruwaito.

Kungiyar a cikin wata sanarwa ta ce zarginta da kisan Gulak daidai yake da aibanta ta lokacin da "'yan ta'adda sanye da kayan jami'an tsaro ke aikata munanan abubuwa a Kudu maso Gabas."

An ruwaito yadda aka kashe Gulak, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Lahadi a Owerri, babban birnin jihar Imo, yayin da ya dawo Abuja

“Ahmed Gulak ya bar dakinsa a Otal din Protea ba tare da ya sanar da 'yan sanda ko hukumomin tsaro ba saboda lamuran tsaro na Kudu maso Gabas da Imo musamman," in ji Premium Times.

KU KARANTA: Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tsohon Hadimin Jonathan, Marigayi Ahmad Gulak

Kungiyar 'Yan Tawaye Ta IPOB Ta Yi Martani Kan Zarginta Da Kashe Ahmed Gulak
Kungiyar 'Yan Tawaye Ta IPOB Ta Yi Martani Kan Zarginta Da Kashe Ahmed Gulak Hoto: punchng.com

Emma Powerful, kakakin IPOB, ya yi watsi da zargin da ke alakanta haramtacciyar kungiyar da mutuwar Gulak kuma ya nemi hukumomin tsaro da su binciki lamarin.

"Kafin alakanta IPOB da aikata laifin kamata ya yi hukumomin tsaro su fara binciken mai masaukin Gulak, Hope Uzodima, da kuma abokan hamayyarsa na siyasa don tabbatar da yiwuwar sa hannunsu."

Kungiyar ta kara da cewa "sai bayan da aka dawo da kasar Biafra" kuma "kashe 'yan siyasa ba ya daga cikin manufofinmu."

Ana yawan zargin kungiyar IPOB da kai munanan hare-hare a yankin kudu maso gabas tun lokacin da ta kaddamar da kungiyar Tsaro ta Gabas (ESN), bangaren ‘yan tawayenta.

KU KARANTA: Shugabannin Kudu Ga Buhari: Najeriya Za Ta Mutu Idan Ba a Gyara Fasalinta Ba

A wani labarin, Biyo bayan bindige tsohon hadimin Jonathan, Ahmed Gulak a jihar Imo, jama'a da dama sun bayyana yanayin da suka ji game da mutuwarsa.

A yau aka samu rahoton cewa an kashe tsohon hadimin a cikin motarsa kuma kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku sharhin jama'a 'yan Najeriya game mutuwar Ahmad Gulak, musamman daga kafar Tuwita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel