Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan

Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan

- Wasu yan bindiga sun harbe wani hamshaƙin ɗan kasuwa har Lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo

- Bayan sun harbi mutumin, maharan sun caka masa wuƙa a ƙirji domin su tabbatar bai tsira da ransa ba

- Kakakin hukumar yan sandan jihar, Mr Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace ana cigaba da Bincike

Wasu yan bindiga da ba'a gano ko su waye ba sun harbe wani ɗan kasuwa har lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Banka Wuta a Sabon Ofishin Hukumar Zaɓe INEC

Legit.ng hausa ta gano cewa yan bindigan sun harbe ɗan kasuwanne ranar Asabar da misalin ƙarfe 8:00 na dare, kamar yadda guardian ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan kasuwan mai suna, Linus Owuamanam, yana cikin tuƙa motar bas yayin da lamarin ya faru dashi a kan hanyar Mokola-Sango Ibadan, jihar Oyo.

Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan
Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

An gano cewa Bayan yan bindigan sun harbi Owuamanam, sai da suka caka masa wuƙa a ɓangaren ƙirjinsa na hagu domin su tabbatar ya sheƙa lahira.

Amma duk da haka an same shi yana numfashi yayin da aka gaggauta kai shi asibiti domin ceto rayuwarsa.

KARANTA ANAN: Ahmed Gulak Ya Fita Masaukinsa Ba Tare da Sanin Mu Ba, Yan Sanda Sun Yi Cikakken Jawabi

A halin yanzu, babu wanda yasan inda ɗayan mutumin da suke tare a cikin motar yake yayin da lamarin ya faru.

Wani mutumi da yazo wucewa ta wurin, shine yaga gawar wanda aka kashe cikin jini, inda yayi gaggawar sanar da ma'aikatan mamacin.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jihar Oyo, Mr Adewale Osifeso, ta wayar tarho ya tabbatar da kisan.

Yace: "Muna gudanar da bincike kan lamarin kuma muna fatan gano waɗan da suka aikata wannan mummunan aikin domin su girbi abinda suka shuka."

A wani labarin Kuma Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Tare da Wasu Mutum Uku

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wani ɗan majalisar dokokin jihar Nasarawa a kan hanyarsa ta zuwa Jos, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban kwamitin hulɗa da jama'a na majalisar, Hon Mohammed Omadefu, shine ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel