Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Banka Wuta a Ofishin Hukumar Zaɓe INEC

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Banka Wuta a Ofishin Hukumar Zaɓe INEC

- Wasu mutane da ba'a san ko su waye ba sun bankawa ofishin INEC wuta a ƙaramar hukuma Njaba dake jihar Imo

- Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da hukumar INEC ta fitar yau Lahadi a shafinta na kafar Sada zumunta

- INEC tace wannan shine karo na takwas da aka kaiwa ofishinta hari a jihar Imo tun bayan kammala zaɓen 2019

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta sanar da cewa an sake banka wuta a wani ofishinta dake jihar Imo.

KARANTA ANAN: Ahmed Gulak Ya Fita Masaukinsa Ba Tare da Sanin Mu Ba, Yan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske

INEC ta bayyana hakane a wani jawabi da ta fitar a shafinta na twitter, tace wasu mutane da ba'a gano ko su waye ba sun cinna wuta a ofishinta dake ƙaramar hukumar Njaba a jihar.

Legit.ng hausa ta gano cewa an ƙona wannan ofishin ne mako ɗaya bayan an ƙona wani ofishin INEC ɗin dake ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise.

Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Banka Wuta a Ofishin Hukumar Zaɓe INEC
Da Ɗuminsa: Yan Bindiga Sun Sake Banka Wuta a Ofishin Hukumar Zaɓe INEC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabin INEC tace: "Kwamishinan INEC na jihar Imo ya kawo mana rahoton cewa, yau Lahadi 30 ga watan Mayu, an banka wuta a ofishinmu dake ƙaramar hukumar Njaba."

"Duk da babu wanda ya rasa rayuwarsa, amma dai an ruguza ginin wajen tare da lalata kayayyakin zaɓen dake ofishin."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Tare da Wasu Mutum Uku

"Wannan harin yazo mako ɗaya bayan an kai ma ofishin mu dake ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise ranar 23 ga watan Mayu, 2021."

Hukumar INEC ta ƙara da cewa wannan shine karo na takwas da aka kiwa ofishinta hari a jihar Imo tun bayan zaɓen 2019.

A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi

Rundunar yan sanda reshen jihar Kogi ta bayyana cewa ta damƙe wasu mutum huɗu ɗauke da makamai a jihar.

Kakakin hukumar na juhar, William Aya, yace jami'an Operation Puff Ander ne suka kama waɗanda ake zargin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel