Ahmed Gulak Ya Fita Masaukinsa Ba Tare da Sanin Mu Ba, Yan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske
- Rundunar yan sandan jihar Imo, ta bayyana cewa marigayi Ahmed Gulak ya fita daga masaukinsa zuwa filin jirgi ba tare da sanin yan sanda ba
- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka halaka hadimin na Jonathan a Owerri
- Kakakin hukumar yan sandan jihar, Bala Elkana, shine ya bayyana haka a wani jawabu da ya fitar, yace yan sanda zasu gudanar da bincike
Rundunar yan sandan jihar Imo, tace jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak, wanda wasu yan bindiga suka kashe a jihar ya fita daga masaukinsa ba tare da jami'an tsaro ba, kamar yadda the nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisa a Jihar Nasarawa Tare da Wasu Mutum Uku
Rundunar ta bayyana haka ne a wani jawabi da kakakin hukumar na jihar Imo, SP Bala Alkana, ya fitar ranar Lahadi.
Legit.ng husa ta kawo muku rahoton cewa, Gulak, jigo a jam'iyyar APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a daren ranar Asabar yayin da yan bindigan suka kashe shi.
Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara ne na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Jawabin hukumar yan sandan yace:
"A ranar 30/05/2021 da misalin ƙarfe 7:20 na safe wasu yan bindiga suka farmaki motar Toyota Camry Cab ɗauke da Ahmed Gulak da kuma wasu mutum biyu da suke kan hanyar su na zuwa filin jirgi."
"Ahmed Gulak ya baro ɗakinsa dake Protea Hotel ba tare da sanarwa hukumar yan sanda ko wasu jami'an tsaro ba, saboda yanayin matsalar tsaron da ake fama da shi a yankin kudu-gabas da jihar Imo kanta."
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Ya Hana Amfani da Babur, Keke Nafef a Faɗin Jiharsa
"Ya bar ɗakinsa ba tare da jami'an tsaro ba yayin da direbansa yabi ta wata hanya da ba'a saba binta ba. Yan bindiga su shida a cikin motar Sienna suka farmake su, suka tsamo Gulak suka kashe shi."
"Kwamishinan yan sandan jihar Imo, CP Abutu Yaro, ya bada umarnin gudanar da bincike a kan kisan, yayin da aka tura jami'an tsaro na musamman su binciko waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin su kamo su." A cewar jawabin.
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Mutum Huɗu Ɗauke da Makamai a Jihar Kogi
Rundunar yan sanda reshen jihar Kogi ta bayyana cewa ta damƙe wasu mutum huɗu ɗauke da makamai a jihar.
Kakakin hukumar na juhar, William Aya, yace jami'an Operation Puff Ander ne suka kama waɗanda ake zargin.
Asali: Legit.ng