Abubuwa 4 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Tsohon Hadimin Jonathan, Marigayi Ahmad Gulak
- A yau ne Najeriya ta yi rashin tsohon mai ba tsohon shugabanta shawari kan harkokin siyasa
- An bindige Ahmad Gulak a jihar Imo akna hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama Sam Mbakwe
- Legit.ng ta tattaro muku bayanai da ya kamata ku sani game da marigayi Ahmad Gulak da jajircewarsa
A yau 30 ga watan Mayu aka harbe fitaccen dan siyasa kuma jigo a jam'iyyar APC, Ahmed Gulak a Owerri, babban birnin jihar Imo, akan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Sam Mbakwe na Kasa da Kasa.
Mutuwar Gulak ta zo ne yayin da ake fama da karuwar rashin tsaro a kudu maso gabas da kudu maso kudu, tare da majiyoyi da suka tabbatar da cewa an kai masa harin ne a cikin motarsa ta Camry mai lamba Texas BFT 2150.
Labarin mutuwarsa ya bayyana ne daga abokin karatunsa, Dakta Umar Ado a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Nigeria Tribune ta ruwaito.
Yayin da kasar ke juyayin rasuwarsa, Legit.ng ta tattaro bayanai game da tsohon hadimin na tsohon Shugaban kasa Jonathan kan harkokin siyasa kamar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina
1. Tsohon mai ba Jonathan shawara na musamman
Marigayi Gulak ya kasance mataimaki na musamman kan harkokin siyasa ga tsohon Shugaban kasa Jonathan kafin sabuwar gwamnati ta karbi mulki a 2015 biyo bayan kada kuri'a da aka yi kuma dimokiradiyya ta kawo shugaba Muhammadu Buhari.
2. Gogaggen dan siyasa
Baya ga kasancewa tsohon mai ba da shawara, Gulak ya kuma kasance tsohon kakakin majalisar dokokin Adamawa. A shekarar 2014, ya bayyana aniyarsa tsayawa takarar gwamna a jihar ta Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP.
3. Rikicin shugabancin PDP na kasa
Wasu gwamnonin jam'iyyar PDP sun taba zargin marigayi tsohon dan majalisar da sanya kansa a matsayin shugaban jam’iyyar ta PDP ta kasa biyo bayan wata baraka a jam’iyyar a shekarar 2016.
4. Sauya sheka
Gulak, tare da rakiyar magoya bayansa, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC a shekarar 2018, sun bayyana dalilin ficewarsu da ganin kokarin gwamnatin Buhari na "lallasa 'yan ta'addan Boko Haram."
KU KARANTA: Mun Biya Fansan N180000000 Kafin a Sako 'Ya'yanmu, Iyayen Daliban Greenfield
A wani labarin, Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, tsohon mai bada shawara na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Owerri, jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.
Gulak, jigo a jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya baro Owerri ne yana hanyarsa na komawa Abuja a daren ranar Asabar yayin da yan bindigan suka kashe shi.
A cewar jaridar Tribune, tsohon abokinsa da suka yi makaranta tare, Dr Umar Ado ne ya bada sanarwar rasuwarsa a ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng