Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina

Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina

- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban makarantar sakandare a wani yankin jihar Katsina

- Rahoto ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun sace shi ne kan hanyarsa ta komawa gida bayan tashi daga aiki

- Sun kira danginsa, amma basu bayyana abinda suke bukata ba, lamarin da ya tada hankalin dangi

Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban makarantar sakandaren Gwamnati ta Ruma da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina, Malam Sa’idu Usha.

Mazauna yankin sun ce an sace Usha ne da yammacin ranar Juma’a bayan an tashi daga makaranta a kan hanyarsa ta komawa Batsari daga Ruma, jaridar Punch ta rwauito.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigan sun bar babur din da Usha ke kai suka shilla dashi cikin dajin.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako

Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Gaba Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina
Wata Sabuwa: 'Yan Bindiga Sun Sace Gaba Shugaban Makarantar Sakandare a Katsina Hoto: africatodaynewsonline.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da 'yan bindiga suka hallaka wani malamin addinin Kirista tare da yin awon gaba da wani a jihar ta Katsina, Vanguard ta ruwaito.

Wani daga cikin mazauna garin ya ce, “An tilasta wa malamin sauka daga babur dinsa aka tafi da shi. An bar babur din a tsakiyar hanya kuma tun daga wancan lokacin, ba mu sake jin komai daga gare shi ba.”

Wata majiyar ta ce, “Masu garkuwar sun kira dangin Malam Sa'idu amma ba su nemi komai ba. Lokacin da muka kira su bayan Sallar Asuba (4 na yamma), sai suka ce mu daina kiransu.”

'Yan bindigar ba su sake tuntubar danginsa ba tun daga lokacin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Katsina, Gambo Isah, bai amsa sakon tes da aka aika masa kan lamarin ba. Bai kuma amsa kira ba.

KU KARANTA: Mun Biya Fansan N180000000 Kafin a Sako 'Ya'yanmu, Iyayen Daliban Greenfield

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji dadi matuka cewa daliban jami’ar Greenfield da aka sako a ranar Asabar yanzu sun dawo gida bayan kwana 40 da suka kwashe a hannun 'yan bindiga.

Har ilayau, Shugaban ya jajantawa iyalan dalibai da ma’aikatan da aka sace a harabar makarantar, Leadership a ruwaito.

Bayan sako daliban kwalejin ilimin noma da gandun daji dake Afaka, shugaban ya roki 'yan bindigan da su hakura su sako sauran daliban na jami'ar Greenfiled, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel