Yanzu Kam Hankalina Ya Kwanta: Buhari Ya Bayyana Farin Ciki Da Sako Daliban Greenfield
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana jin dadinsa ga sako daliban jami'ar Greenfield
- Shugaban ya ce Najeriya ba za ta amince da ci gaba da satar mutane da aikata laifuka ba
- Hakazalika ya jajantawa iyaye da iyalan wadanda aka sace a harabar jami'ar ta Greenfield
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji dadi matuka cewa daliban jami’ar Greenfield da aka sako a ranar Asabar yanzu sun dawo gida bayan kwana 40 da suka kwashe a hannun 'yan bindiga.
Har ilayau, Shugaban ya jajantawa iyalan dalibai da ma’aikatan da aka sace a harabar makarantar, Leadership a ruwaito.
Bayan sako daliban kwalejin ilimin noma da gandun daji dake Afaka, shugaban ya roki 'yan bindigan da su hakura su sako sauran daliban na jami'ar Greenfiled, Premium Times ta ruwaito.
KU KARANTA: Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i
Shugaban ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatocin Jihohi domin kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi a duk fadin kasar, gami da cibiyoyin ilimi da sauran wuraren.
Satar mutane babban laifi ne da kuma take hakkin 'yan kasa na gari; Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa satar mutane da duk wasu nau'ikan aikata laifuka zasu ci gaba da fuskantar tofin Allah-tsine, kuma ba za a amince dashi a Najeriya ba.
KU KARANTA: Kungiyar Kiristoci Ga Sanataoci: Ba Ruwanmu Da Addini a Najeriya Balle Shari'a
A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya aika sako zuwa ga dalibai 14 da aka sako na Jami’ar Greenfield, wadanda suka share kwanaki a hannun 'yan bindiga.
A cikin wata sanarwa a daren Asabar da kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar, El-Rufai ya yi maraba da labarin sakin daliban.
"Gwamna Nasir El-Rufai ya yi maraba da labarin sakin daliban, kuma ya isar musu da jaje da karfafa gwiwa sakamakon mummunan halin da suka shiga.
Asali: Legit.ng