Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako

Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana jin dadinsa da sako daliban jami'ar Greenfield da aka yi

- Ya tura sakon jaje da garesu, tare da karfafa musu gwiwa a rayuwarsu ta nan gaba da nasara

- Ya kuma bukaci daliban da cewa su manta komai tunda komai ya wuce, hakan zai taimakesu

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya aika sako zuwa ga dalibai 14 da aka sako na Jami’ar Greenfield, wadanda suka share kwanaki a hannun 'yan bindiga.

A cikin wata sanarwa a daren Asabar da kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar, El-Rufai ya yi maraba da labarin sakin daliban.

KU KARANTA: Lai Mohammed Ga ’Yan Najeriya: Ku Kwantar da Hankali, Najeriya Na Cikin Aminci

Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako
Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako Hoto: bbc.com
Asali: UGC

"Gwamna Nasir El-Rufai ya yi maraba da labarin sakin daliban, kuma ya isar musu da jaje da karfafa gwiwa sakamakon mummunan halin da suka shiga.

"Ya ba su tabbacin cewa bacin ran da suka shiga na ‘yan makonnin da suka gabata, yanzu ya wuce, zai sanya koma baya ga kyawawan nasarori a rayuwarsu, kamar yadda yake yi musu fatan alheri a nan gaba."

A jiya ne aka sako daliban 14 bayan share makwanni a hannun 'yan bindigan da suka yi awon gaba dasu a harabar makaranta.

KU KARANTA: Kungiyar Kiristoci Ga Sanataoci: Ba Ruwanmu Da Addini a Najeriya Balle Shari'a

A wani labarin, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Asabar ya tuna yadda wani gwamna ya shafa masa cutar COVID-19 shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito.

El-Rufai, yayin da yake jawabi a laccar Ahmadu Bello Foundation ta bakwai a Kaduna ranar Asabar, ya kuma ce akalla mutane 50,000 ne cutar za ta kashe a shekarar da ta gabata idan da ba a sanya takunkumi ba.

Gwamnan, a ranar 26 ga Maris, 2020, ya sanya takunkumi a jihar Kaduna, bayan barkewar cutar COVID-19 ya kuma dage dokar a ranar 9 ga Yunin, 2020, bayan kwanaki 75.

Asali: Legit.ng

Online view pixel