Mun Biya Fansan N180000000 Kafin a Sako 'Ya'yanmu, Iyayen Daliban Greenfield
- Iyayen daliban jami'ar Grrenfield da 'yan bindiga suka sako jiya Asabar sun bayyana yadda aka yi aka sako 'ya'yansu
- Sun ce su suka biya kudin fansa kimanin N180m kafin 'yan bindigan su amince su sako musu 'ya'yansu
- Sun kuma koka kan cewa, gwamnati ba ta tura dan sanda ko daya ba domin duba tare da kwato musu 'ya'yan nasu
A jiya Asabar ne 'yan bindiga suka sako daliban jami'ar Greenfield dake jihar Kaduna, wadanda suka sace kwanaki 40 da suka gabata.
Iyayane daliban sun bayyana yadda aka yi aka sako musu 'ya'yansu da suka share kwanaki a cikin daji tare da 'yan bindiga.
A cewar iyayen, an sako yaran ne bayan biyan kudin fansa N180m ga masu satar mutanen, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i
Sun bayyana cewa sun sayar da kadarorinsu don tara kudin fansar N180m da aka biya 'yan bindigar da suka mamaye harabar jami’ar a ranar 20 ga Afrilu kuma suka tafi da dalibai 18 da ma’aikatan makarantar guda uku.
Daya daga cikin iyayen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “mun biya Naira miliyan 180; abin da suka karba kenan daga gare mu ba tare da taimakon wata gwamnati ba.
“Mu, iyaye, mu muka biya. Gwamnati ba ta aika dan sanda ko daya ba don ya dawo mana da yaranmu daga masu garkuwar.”
Wata mahaifiya da aka ga tana kuka ta ce sun kuma ba 'yan bindigan babura a matsayin kudin fansa.
Gwamnatin jihar Kaduna da take tabbatar da sakin daliban, ba ta bayyana yadda aka yi aka kubutar dasu ba, kawai cewa ta yi:
”Daliban da aka sace na jami’ar Greenfield, wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su, sun kubuta daga wadanda suka sace su.
“Wannan rahoto ne ga Gwamnatin Jihar Kaduna daga hukumomin tsaro." Vanguard News ta ruwaito.
KU KARANTA: Gwamna El-Rufai Ya Aika Sako Zuwa Ga Daliban Jami'ar Greenfield Da Aka Sako
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ji dadi matuka cewa daliban jami’ar Greenfield da aka sako a ranar Asabar yanzu sun dawo gida bayan kwana 40 da suka kwashe a hannun 'yan bindiga.
Har ilayau, Shugaban ya jajantawa iyalan dalibai da ma’aikatan da aka sace a harabar makarantar, Leadership a ruwaito.
Bayan sako daliban kwalejin ilimin noma da gandun daji dake Afaka, shugaban ya roki 'yan bindigan da su hakura su sako sauran daliban na jami'ar Greenfiled, Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng