Da duminsa: Tsagerun yan bindiga sun kuma afkawa ofishin yan sanda, sun kashe jami'ai 3

Da duminsa: Tsagerun yan bindiga sun kuma afkawa ofishin yan sanda, sun kashe jami'ai 3

- Kai hari ofishin yan sanda ya fara zama ruwan dare a Najeriya

- Wannan karo, an yi rashin akalla jami'an yan sanda uku

- Ana zargin yan ta'addan IPOB/ESn da kai hare-hare a yankin kudu maso gabashin Najeriya

Jami'an yan sanda uku na ofishin Umutu dake karamar hukumar Ukwani a jihar Delta sun rasa rayukansu cikin daren Juma'a, 28 ga watan Mayu, 2021.

Hakan ya biyo bayan harin da wasu yan bindiga suka kai ofishin yan sandan misalin karfe 1:30 na dare.

A cewar rahoton TVCNews, Kakakin hukumar yan sandan jihar, Edafe Bright, ya ce yan bindigan sun budewa yan sandan wuta inda suka hallaka uku.

Ya kara da cewa yan sanda sun samu nasarar kashe mutum biyu cikinsu kuma wasu da dama sun jikkata.

A cewarsa, yan bindigan sun tafi da gawawwakin abokansu.

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Da duminsa: Tsagerun yan bindiga sun kuma afkawa ofishin yan sanda, sun kashe jami'ai 3
Da duminsa: Tsagerun yan bindiga sun kuma afkawa ofishin yan sanda, sun kashe jami'ai 3
Asali: Original

DUBA NAN: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

A bangare guda, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, a ranar Laraba, ya ce yan Najeriya su daina yaudarar kansu cewa abubuwa na tafiya daidai a Najeriya.

Sultan Saad ya bayyana hakan ne a taron tattauna matsalar tsaro dake gudana a Abuja, rahoton Channels.

"Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwa na tafiya daidai, abubuwa sun tabarbare. Mun san hakan, kuma muna gani," Sultan yace.

"Abubuwa sun yi muni yanzu. Ba ka bukatar wani ya fada maka Najeriya na cikin halin ha'ula'i kuma wannan shine gaskiya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng