Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce

Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce

- Wani tsohon hoton shugaban kasar Najeriya lokacin da yake matashi ya bayyana a yanar gizo kuma ya ya haifar da cece kuce a kafafen sada zumunta

- A cikin hoton, an ga matashi Buhari yana rawa tare da wata farar mace ba takalmi yayinda sauran matan ke kallo

- Mutane da yawa sun nuna sha’awarsu ga hoton yayinda wasu ke jayayya cewa ya fi zama dan gaye a lokacin samartakarsa fiye da yadda yake yanzu

Wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.

Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce
Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce Hoto: Ayo Ojeniyi
Asali: Facebook

Da yake wallafa hoton, ya rubuta cewa:

PMB ya kasance dan sharholiya sosai yayin da yake tasowa. A zamanin nan, ya kame kansa !!! Dube shi yana shanawa a wani liyafa lokacin da yake saurayi !!!!

Buhari ya kasance dauke da murmushi yayin da suke rawa inda sauran matan da ke wurin suke kallo.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji

Dubi wallafar da yayi a ƙasa:

Mutane da yawa sun nuna farin ciki yayin da suke tsammanin cewa shugaban kasar ya fi shanawa a zamanin da yake tasowa idan aka kwatanta da yanzu.

Wasu suna mamakin dalilin da yasa suka kasance ba tare da takalmi ba.

Ayoola Akinkumi Olamide ya rubuta:

Mai shanawa? 1 daga cikin 50. Bayan barinsa mulki a 1985 sau nawa ya yi mu'amala da mutane a wajen Arewarsa. Lokaci guda da ya ziyarci Kudu maso Yamma shi ne lokacin da ya zo don karbar cin mutunci daga Lam Adesina. Wanene abokinsa na kut da kut a Kudancin kasar gaba daya kafin 2007? Ba komai ba ne shi face kifin rijiya har zuwa lokacin.

Adams Yusuf ya ce:

Ka zama mai tawali'u da kuma nutsuwa a lokacin da kake tsufa.
Kuma fa sauran kyawawan matan suna jiransa ya yi rawa tare da su. Lallai ma.

Segun Fagbemi ya ce:

Da ya ci gaba da ritaya.

Damuwar Najeriya ta yau ta wuce karfi da kuzarinsa.

A wani labarin, a ranar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2021, tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya caccaki hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Olusegun Osoba ya ja-kunnen mai magana a madadin shugaban Najeriyar ya bi sannu a hankali ka da jawabinsa ya rika sha ban-bam da na mai gidansa.

Jagoran na APC ya gargadi Garba Shehu a kan yin kalaman da suka bambanta da ra’ayin mai girma Muhammadu Buhari da matsayar jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng