Yan majalisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya

Yan majalisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya

- Tun 2018 da Najeriya tayi odan jiragen yaki, ana shirin kawosu yanzu

- Yan majalisar dokokin sun garzaya Amurka don ganin jiragen

- Fadar shugaban kasa ta ce za'a kawo shida cikin 12 a watan Yuli

Tawagar yan majalisar dokokin Najeriya sun kai ziyara kasar Amurka domin ganewa idanwansu sabbin jiragen yaki na A-29 Super Tucano da gwamnatin Najeriya tayi oda tun 2018.

A Febrairun 2018, shugaba Muhammadu Buhari ya bada kudi $469.4 million don sayan jirage Tucano guda 12 domin yaki da yan ta'adda.

Yan majalisar da wasu jami'an hukumar mayakan sama sun kai ziyara kamfanin ne domin ganin yadda ayyuka ke gudana kan odan da Najeriya tayi.

Fadar shugaban kasa, a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris ta ce shida cikin sabbin jiragen yaki 12 da gwamnati tayi oda daga kasar Amurka za su iso a watan yuli, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki mai taken 'Jiragen Super Tucanon Najeriya zasu iso tsakiyar watan Yuli 2021.'

Yace: "Shida cikin jiragen Super Tucano 12 na kan hanyar zuwa tsakiyar Yuli 2021. Akwai matukan jirgin Najeriya 14 dake horo a Moody Air Force Base dake Georgia."

Kalli hotunansu:

Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Asali: Twitter

Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Asali: Twitter

Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Yan majlisa sun dira Amurka don ganin jiragen yakin da Najeriya ta saya
Asali: Twitter

DUBA NAN: Nan da shekara 2, har yan adawa sai sun jinjinawa shugaba Buhari: Fadar Shugaban kasa

A bangare guda, gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Faruk Yahaya a matsayin sabon shugaban hafsan soji.

Gwamnatin ta yi wannan bayanin ne ta bakin Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi-Magashi (mai ritaya) a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 28 ga watan Mayu.

Sanarwar da mai magana da yawun ministan, Mohammad Abdulkadri ya fitar, kuma Legit.ng ta gani, ta ce Shugaba Buhari ya yi zabin ne saboda kishin kasa da kuma bukatar hadin kan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel