Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu

Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu

- Hukumomi a Jihar Kebbi sun tabbatar da gano gawarwakin fasinja 76 bayan hatsarin kwalekwalen da ya auku

- Hukumar NIWA ta sanar da hakan da kuma cewa tana ci gaba da aikin ceto, tun bayan kifewar jirgin mai dauke da fasinja kusan 200 a kauyen Tsohuwar Labata

- Shugaban hukumar a jihar Kebbi, Birma Yusuf ya ce Hukumar na da kwarewa wajen gudanar da aikin ceto, amma rashin ingancin kayan aiki na kawo musu cikas

Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Najeriya (NIWA) ta ce kawo yanzu an gano gawarwaki 76 daga hatsarin jirgin ruwan da ya faru a kauyen Tshohuwar Labata da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi.

Manajan NIWA a jihar, Birma Yusuf, ne ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Juma’a, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken saboda ana sa ran za a gano sauran gawarwakin.

KU KARANTA KUMA: Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kai wa Buhari ziyara a Abuja

Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu
Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Gawarwakin da aka gano sun yi ta yawo a gabar Kogin Neja kusa da inda mummunan hatsarin ya auku.

Yusuf ya koka kan rashin isasshen kayan aikin hukumar don aikin ceto.

Ya ce hukumar na da kwarewar aikin ceto sannan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta taimaka wa hukumar da jiragen ruwan domin inganta ayyukan su.

Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 76. A koyaushe muna zargin masu gudanar da kwalekwale da yin lodin da ya zarta kima da kuma amfani da tsofaffin jiragen ruwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Manjo Janar Farouq Yahaya ya kama aiki a matsayin Shugaban hafsan soji na 22

Zuwa daren Juma’a masu aikin ceto sun yi nasarar ceto kimanin mutum 30 da ransu daga cikin fasinjoji jirgin.

Suleman Bobo daya daga cikin masu aikin kuma Shugaban matasa garin Warra ya tabbatar wa da wakilin jaridar Aminiya.

Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

Da farko Legit.ng ta kawo cewa Fasinjoji masu tarin yawa sun nitse a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Laraba bayan tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Neja, jami'i mazaunin yankin ya tabbatar.

Jirgin ruwa da ya bar jihar Kebbi yana tunkarar yankin arewa maso yammacin jihar Kebbi ya fashe sannan ya nitse, Abdullahi Buhari Wara, hakimin Ngaski ya tabbatar.

Tuni dai masu ceto suka fada kogin amma mutum 22 tare da gawar mutum daya suka iya tsamowa, Wara yace a yanzu kusan fasinjoji 140 ne babu duriyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel