Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Umahi Ya Sauke Masu Riƙe da Muƙaman Siyasa a Jiharsa
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya soke majalisar zartarwa na jiharsa nan take, The Nation ta ruwaito.
Sakataren gwamnatin jihar, SSG, Keneth Ugbala ne ya sanar da soke majalisar bayan taronta a ranar Juma'a a Abakaliki.
Amma ya ce akwai wasu masu rike da muhimman mukamai da abin bai shafe su ba.
DUBA WANNAN: Masu Zanga-Zanga Sun Tafi Da Gawarwaki Zuwa Fadar Sarkin Zurmi a Zamfara
Wadanda abin bai shafa ba sun hada da SSG, Antoni Janar, Kwmishinan Shari'a, Cletus Oke; Kwamishinan Kudi, Orlando Nweze da kwamishinan Labarai, Uchena Orji.
Saura sun hada da kwamishinan Tabbatar da Lafiyar iyakoki, Stanley Okoro Emegha; Babban Mai bada shawara kan saka hannun jari, Chioma Nweze da kwamishinan babban birnin jiha, Onyekachi Nwebonyi.
Kwamishinan Ayyukan tituna, Nweze Kings da takararsa na ayyuka, Ogbonnaya Obasi da SSA kan Jin Dadi da Harkokin Addinai Rabaran Abraham Nwali suma suna nan kan aikinsu.
KU KARANTA: Nigeria Ba Za Ta Taɓa Zama Ƙasar Musulunci Ba, Inji Jikan Shagari
Masu taimakawa na musamman ga gwamna na ofishin mataimakin gwamna, babban birni, Kudi, Wuraren shakatawa da Kiwon Lafiya suma suna nan kan aikinsu.
Dukkan masu taimakawa gwamnan na kansa suma abin bai shafe su ba.
Ugala ya ce an sauke masu mukaman ne domin gwamnati ta yi bita kan ayyukansu.
Ya ce sauke sun a yanzu baya nufin tasu ta zo karshe yana mai cewa akwai yiwuwar wasu daga cikinsu su koma aikinsu bayan bitar.
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.
Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.
Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.
Asali: Legit.ng