Jonathan ya shiga-ya fita har sai da Sojojin tawaye suka fito da Shugabannin Mali da suka tsare

Jonathan ya shiga-ya fita har sai da Sojojin tawaye suka fito da Shugabannin Mali da suka tsare

- Goodluck Jonathan ya taimaka wajen sakin Bah Ndaw da Moctar Ouane a Mali

- Tsohon Shugaban kasar Najeriya ne ya jagoranci kwamitin sulhu na ECOWAS

- A dalilin kokarin da tawagar Jonathan ta yi a Mali aka saki shugabannin kasar

Yunkurin sasancin da tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan yake yi wajen kawo karshen rikicin kasar Mali, ya na haifar da ‘da mai ido.

Jaridar Punch ta ce wannan kokari na Goodluck Jonathan ya yi nasarar fito da shugaban rikon kwarya da Firayim Ministan Mali da sojoji suka tsare.

A wani jawabi da ya fito daga ofishin yada labarai na Goodluck Jonathan a ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu, 2021, an yi bayanin rawar ganin da ya taka.

KU KARANTA: Tawagar Goodluck Jonathan ta gana da Shugaban Ƙasar Mali

An yi wa wannan jawabi take da ‘Mali’s President, Prime Minister released after Jonathan’s mediation’, hakan ya na nufin Dr. Jonathan sun sa hannu.

Jawabin ya bayyana cewa sojojin Mali sun saki shugaban rikon kwarya, Bah Ndaw, da Firayim Minista, Moctar Ouane, bayan sa bakin Goodluck Jonathan.

This Day ta ce tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, shi ne ya jagoranci tawagar sulhun da kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta tura Mali.

A ranar Talata ne Jonathan ya isa garin Bamako, Mali, inda ya gana da shugabannin sojoji da sauran masu ruwa da tsaki, ya bukaci a fito da shugabannin.

Jonathan ya shiga-ya fita har sai da Sojojin tawaye suka fito da Shugabannin Mali da suka tsare
Jonathan a Mali Hoto: www.theafricareport.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Najeriya, ECOWAS sun yi tir da hambarar da Gwamnati a Mali

“Shugaban sulhun da tawagarsa sun samu tabbacin shugabannin sojoji a kan sakin Ndaw da Ouane, bayan sun kai masu ziyara a barikin Katti, kusa da Bamako.”

“Kafin ya hadu da shugaban kasa da Firayim Ministan, Jonathan ya zauna da Kanal Assimi Goita, inda ya bukaci a fito da shugabannin kasar ba tare da wata-wata ba.”

Dr. Jonathan ya yi kira ga Assimi Goita ya yi abin da zai kawo zaman lafiya da kafa mulkin farar hula.

A halin yanzu, sojojin tawayen kasar Mali sun saki shugaba Bah Ndaw da Moctar Ouane da aka daure. An yi hakan ne a sakamakon sa bakin tawagar ta ECOWAS.

A makon nan ne wani hadimin sabon shugaban Mali mai-ci ya ce shugaban kasa da Firayim Ministansa sun yi murabus daga kan kujerunsu bayan fitowarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng