Matsalar Tsaro: Mun Cafke Masu Aikata Manyan Laifuka Sama da 1,000 Cikin Wata Ɗaya Kacal, IGP
- Hukumar yan sanda ta ƙasa ta bayyana nasarar da IGP ya samu tun bayan shigars Ofis a watan Afrilu
- Hukumar tace ta kama mutum sama da 1,000 da zargin aikata manyan laifuka a sassa daban-daban na ƙasar nan
- Hakanan, jami'an hukumar sun kuɓutar da mutum 152 da aka sace tare da kwato bindigu 413 daga hannun yan ta'adda
Hukumar yan sanda ta ƙasa (NPF) ta bayyana cewa ta cafke manyan masu laifuka sama da 1,000 da take zargi da hannu a rikice-rikice a faɗin ƙasar nan cikin wata ɗaya.
KARANTA ANAN: Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu
Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Alƙali Baba, shine ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Alhamis, kamar yadda the caple ta ruwaito.
A ranar 6 ga watan Afrilu, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Baba a matsayin muƙaddashin sufeta janar na ƙasa.
Da yake jawabi kan nasarorin da ya samu zuwa yanzun, Usman Baba yace an kama waɗanda ake zargin ne daga watan Afrilu zuwa Mayu 2021.
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina
Yace: "Mun kama mutum 398 da zargin aikata fashi da makami, mutum 258 da zargin aikata laifukan dA suka shafi ƙungiyoyin asiri."
"Hakanan kuma mun kama mutum 222 da laifin kisan kai, yan bindiga 202, da kuma masu garkuwa da mutane 86."
IGP ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kama ɗin akwai waɗanda keda hannu a harin da aka kaiwa gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.
Hukumar tace ta kuɓutar da mutum 152 da aka sace, yayin da ta kwato bindigu 423 da alburusai 10,120 a tsakanin wannan lokacin.
A wani labarin Mun Cafke Duk Wani Mai Hannu a Harin da Aka Kaiwa Gwamnan Benuwai, IGP
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta kama dukkan masu hannu a harin da aka kaiwa gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.
Muƙaddashin sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba, Shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.
Asali: Legit.ng