Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu

Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu

- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu mai binta bashi daga cikin ma'aikatan Npower da suka gama aiki

- Ministar ma'aikatar jin kai da walwala, Sadiya Farouk, itace ta bayyana haka, tace an biya ko wane ma'aikaci haƙƙinsa

- Ta kuma ƙara da cewa yanzun haka ana cigaba da tantance ma'aikatan da za'a ɗauka a runkunin C

Gwamnatin tarayya tace ta biya dukkan ma'aikatan N-Power haƙƙinsu da aka riƙe a cewar ministan jin kai, Sadiya Farouk, kamar yadda The nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Fatattaki Yan Bindiga Daga Kai Hari, Ta Sheƙe 4 a Jihar Katsina

Kusan ma'aikatan npower 14,000 daga rukunin A da B, waɗanda suka gama aikin su a shekarar data gabata ne suke bin gwamnati albashin su na watanni 4.

Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu
Minista Tayi Magana Kan Shirin N-Power, Tace an Biya Dukkan Ma’aikata Haƙkinsu Hoto: @Sadiya_Farouq
Asali: Twitter

Ministar ma'aikatar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouk, ta bada umarnin duk wanda abun ya shafa ya kai rahoto ga shugaban npower na jiharsa domin tantancewa.

Ministan ta bada wannan umarnin ne a wani ɓangare na ƙoƙarinta wajen ganin an biya waɗanda aka riƙewa albashinsu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar PDP

Yayin da take jawabi a wurin wani taron ƙara wa juna sani da ma'aikatarta ta shirya kan 'rahotannin kafafen sada zumunta' Minista tace:

"Bana tunanin muna da wata matsala da ma'aikatan npower, mun riga mun warware komai tsakanin mu da Akanta janar na ƙasa (AGF)."

"Ya ɗauke mu dogon lokaci amma daga ƙarshe mun cinma manufa, Mun biya dukkan ma'aikatan npower bayan dogon bincike."

"Yanzun ma'aikatar mu zata cigaba da aikin ɗaukar ma'aikata a shirin npower na rukunin C, Mun kasa shi zuwa gida biyu, zamu ɗauki mutum 500,000 da farko Sannan daga baya mu ƙara kamar haka."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Sake Taɓo Hanyar Magance Matsalar Tsaro, Yace Yana Buƙatar Haɗin Kan Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana cewa magance matsalar tsaron da ƙasar nan ke fama da ita ya rataya a wuyan kowa.

Shugaban yace sai yan Najeriya sun bada haɗin kai da taimakawa gwamnati sannan zata iya samun nasara a wannan yaƙin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262