Manjo-Janar Yayaha: Jerin Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar Tun Daga Shekarar 1999

Manjo-Janar Yayaha: Jerin Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar Tun Daga Shekarar 1999

- A yau Alhamis, 27 ga watan Mayu ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin Shugaban hafsan sojan kasar

- Tun daga shekarar 1999 lokacin da kasar ta koma mulkin farar hula, an yi shugabannin soji 10 a kasar ciki harda sabon nadin da aka yi a yau

- Manjo Janar Farouk dai ya maye gurbin marigayi Shugaban hafsan sojan kasar (COAS) Ibrahim Attahiru ne

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi Shugaban hafsan sojan kasar (COAS) Ibrahim Attahiru.

Bayan nadin nasa, Legit.ng a cikin wannan rahoton ya kawo muku cikakken jerin sunayen COAS tun daga 1999 lokacin da Najeriya ta koma kan mulkin farar hula.

Kamar yadda Legit.ng ta gano, Shugabannin Najeriya tun daga 1999 sun nada shugabannin soji tara, wanda ya kawo jimillar zuwa 10 tare da wannan sabon nadin.

KU KARANTA KUMA: Bayan Nada Farouk Yahaya, Ana Kyautata Zaton Manjo-Janar 10 Za Su Yi Ritayar Dole

1. Laftanar Janar Victor Malu - Mayu 1999 - Afrilu 2001

2. Laftanar Janar Alexander Ogomudia - Afrilu 2001 - Yuni 2003

3. Laftanar Janar Martin Luther Agwai - Yuni 2003 - Yuni 2006

Manjo-Janar Yayaha: Jerin Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar Tun Daga Shekarar 1999
Manjo-Janar Yayaha: Jerin Manyan Hafsoshin Sojojin Kasar Tun Daga Shekarar 1999 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

4. Laftanar Janar Owoye Andrew Azazi - 1 Yuni 2006 - Mayu 2007

5. Laftanar Janar Luka Yusuf - Yuni 2007 - Agusta 2008

6. Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau - Agusta 2008 - Satumba 2010

KU KARANTA KUMA: Sabon Nadi: Sharhin 'Yan Najeriya Game da Nada Manjo-Janar Farouk Yahaya

7. Laftanar Janar Azubuike Ihejirika - Satumba 2010 - Janairu 2014 8. Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai - Yuli 2015 - 26 Janairu 2021

9. Laftanar Janar Attahiru Ibrahim - 26 Janairu 2021 zuwa 21 May 2021

A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Farouk Yahaya a matsayin shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya.

Yahaya, mai mukamin manjo janar zai maye gurbin marigayi Attahiru Ibrahim a take.

Kafin nadinsa, Yahaya shine babban kwamandan Div 1 na rundunar sojin kasa ta Najeriya.

Kamar yadda hedkwatar dakarun sojin kasa ta Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon shugaban sojin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel