Ministan Buhari: Idan Talakawa Suka Nemi Na Tsaya Takarar Shugabancin 2023, Zan Yi
- Wani daga cikin ministocin Buhari ya bayyana matsayarsa kan tsayawa takara a zaben 2023
- A cewarsa, yana duba bukatar al'umma ne ba wai son zuciyarsa ba, don haka bai da amsar tsayawa
- 'Yan siyasa da dama a Najeriya na harin kujerar shugabancin kasa a zaben shekara ta 2023 mai zuwa
Rauf Aregbesola, ministan cikin gida, ya ce yana cikin "gungun 'yan siyasa masu himma da taka-tsantsan" wadanda ba za su yi tsalle kawai su shiga takarar shugabancin kasa a 2023 ba tare da yin la'akari da kyau ba.
Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron tattaunawa mai taken: "Afirka: Bijiro da Tambayoyi kan Shugabanci".
Ministan, lokacin da wani da ya halarci taron ya tambaye shi ko yana da shirin tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a 2023, cewa ya yi ba shi da amsa ga tambayar, TheCable ta ruwaito.
KU KARANTA: Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi
“Ba ni da amsa a kan hakan. Ina cikin gungun 'yan siyasa masu himma, taka-tsantsan, wadanda ba da son kansu kawai suke yin tsalle su bi son zuciyarsu ba, ban taba yin hakan ba a baya kuma ba zan fara hakan ba a yanzu,” inji shi.
Jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya na ci gaba da nuna sha'awarsu ga kujerar shugaban kasa a Najeriya, yayin da aka fara ganin fastocin dauke da hotunan wasu da dama na yakin neman zabe a 2023.
Ba a bar Bukola Saraki a baya ba, domin kuwa a watan Afrilu an ga hotunansa na yakin neman takarar shugabanci a 2023 a wasu sassan babban birnin tarayya Abuja, Vanguard ta ruwaito.
Amma cikin hanzari, mai magana da yawun Saraki, Yusuf Olaniyonu, ya yi martani yana cewa, "ba mu san komai game da fastocin ba."
KU KARANTA: Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi
A wani labarin, Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya ce shi kadai ne gwamnan Najeriya da ba ya karbar albashi duk wata, PM News ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana cewa bayan an cire haraji daga albashinsa, sai ya tura ragowar kudin zuwa gidajen marasa galihu don kula da su.
Ya kara da cewa ya kasance yana yiwa jihar aiki ne.
Asali: Legit.ng