Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi

Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi

- Kwamishinan 'yan sanda ya bayyana yadda jihar Kano ta shirya karbar Fulani makiyaya a jihar

- Ya ce sam jihar ba za ta amince da fulanin da za su shigo ba tare da bin ka'idar da aka sanya ba

- A cewarsa, dole ne Fulanin su ba da takardar izini daga jihar da suka baro kafin a barsu su zauna a Kano

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Sama’ila Dikko, ya ce dole ne Fulani makiyaya da ke shigowa jihar ta Kano su samu izini daga rundunar 'yan sanda ta jihar da za su baro zuwa Kano.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron gaggawa na tsaro tare da shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa a ranar Laraba, Mista Dikko ya ce duk wani Bafulatani makiyayi da ya shigo Kano ba tare da izinin ba za a mai dashi in da ya fito, in ji Daily Nigerian.

Ya ce wannan shawarar na daga cikin tsare-tsaren tsaro da rundunarsa ta yi a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

KU KARANTA: Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi

Duk Makiyayin da Ya Shigo Kano Ba Tare da Izini Ba Za a Mai Dashi in da Ya Fito, ’Yan Sanda
Duk Makiyayin da Ya Shigo Kano Ba Tare da Izini Ba Za a Mai Dashi in da Ya Fito, ’Yan Sanda Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce bayan jin labarin shigowar Fulani zuwa jihar ta Kano, rundunar 'yan sanda ta yi kokarin zaman tattaunawa da sauran hukumonin tsaro a jihar bayan ta gana da shugabannin Fulani.

“A taron da na yi a ofishina da safiyar yau tare da shugabannin Fulani daga Kaduna, Katsina da Jigawa, na nemi su ba mu duk wani bayani da za mu toshe duk wanda zai shigo ba tare da izini na dole daga ;yan sandan jihar da suka baro ba.

“Don haka, dole ne a samu wasika, wacce ke nuna cewa za su zo Kano daga wata jihar. Don haka, duk wanda ya zo ba tare da izini daga tsarin 'yan sanda ba, daga jihar da ya baro, ba shakka za a tsayar da shi a mai da shi zuwa inda ya fito.

“Ba za mu yarda da duk wanda ya zo nan ba bisa doka ba. Ba lallai mu san wadanne irin mutane bane. Suna iya zama masu aikata laifi. Suna iya zama 'yan bindiga ko wasu mugayen mutane. Don haka, ba za mu yarda da shi a nan Kano ba," ya jaddada.

Fulani makiyaya na fuskantar cece-kuce kan kasancewarsu da daukar shanu daga jihohin arewa zuwa kudancin Najeriya.

Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na kasa (MACBAN), Sanata Walid Jibrin, ya ce dokar hana kiwo a fili za ta taimaka wajen magance rikicin manoma da makiyaya a kasar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Hotuna da Bidiyon Yaron Da Ya Tashi a Daji Yana Cin Ciyawa Ya Ba Da Mamaki

A wani labarin, Mahukunta a jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil a Jihar Kano ta ce za ta dauki "mummunan mataki" kan daliban da suka cin zarafin wata daliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata ta shafin Tuwita, shugaban sashen harkokin dalibai ya nemi afuwar dalibar sannan ya bukaci ta shigar da kara a hukumance domin neman hakkinta da aka take.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata daliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami'ar ne ta Wudil.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.