Shugaba Buhari Ya Sake Taɓo Hanyar Magance Matsalar Tsaro, Yace Yana Buƙatar Haɗin Kan Yan Najeriya
- Shugaba Buhari ya bayyana cewa magance matsalar tsaron da ƙasar nan ke fama da ita ya rataya a wuyan kowa
- Shugaban yace sai yan Najeriya sun bada haɗin kai da taimakawa gwamnati sannan zata iya samun nasara a wannan yaƙin
- Shugaban ya jinjina wa yan Majalisa bisa shirya taro kan tsaro a dai-dai lokacin da ƙasar ke buƙatar hakan biyo bayan rasuwar COAS Ibrahim Attahiru
Shugaba Muhammadu Buhari yace magance ƙalubalen tsaro a ƙasar nan yana buƙatar haɗin kai da taimakon yan Najeriya baki ɗaya, kamar yadda Vangurd ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Tawagar Goodluck Jonathan Ta Gana da Shugaban Ƙasar Mali da Aka Hamɓarar
Buhari ya faɗi haka ne a wajen buɗe taron kwana 4 da majalisar wakilan Najeriya ta shirya domin ji ta bakin jama'a kan tsaron ƙasa ranar Laraba a Abuja, kmar yadda leadership ta ruwaito.
Buhari ya jinjinawa majalisar bisa shirya taron da zai baiwa masu ruwa da tsaki damar tofa albarkacin bakin su kan batun da ya dabai-baye ƙasar nan da kuma yadda za'a matsa gaba.
Shugaba Buhari, wanda sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya wakilta yace ƙalubalen tsaro ya zama babban abinda ya damu duniya, nahiyoyi da ƙasashe.
Yace: "Najeriya ta haɗa iyaka da Benin, Kamaru, Chadi, da Nijar, sannan kuma ta haɗa iyakar ruwa da Equatorial Guanine, Ghana, Sao Tome da Principe."
"Ƙalubalen dake waɗannan iyakoki kaɗai sun isa su jawo matsalar tsaron ƙasar mu ya zama wani babban lamari, rashin tabbas a rikicin tafkin Chaɗi kaɗai yana buƙatar a maida hankali a kanshi."
KARANTA ANAN: Ya Kamata a Baiwa Jihohi Damar Yanke Kananan Hukumomi Nawa Zasu Iya Ɗauka, El-Rufa'i
"Ƙasar mu na fama da matsalolin tsaro kala daban-daban a dukkan ɓangarorin ƙasar nan, magance su da dawo da zaman lafiya yana wuyan kowane ɗan Najeriya; masu riƙe da madafun iko da kuma waɗanda ake mulka."
Buhari ya ƙara da cewa taron yazo a dai-dai yayin da ƙasar ke juyayin mutuwar shugaban rundunar sojin ƙasa, Lt.-Gen. Ibrahim Attahiru, tare da wasu manyan Jami'an soji, waɗanda suka rasa ransu a hatsarin jirgi.
Mutuwar su babban rashi ne ga ƙasa, jami'an rundunar soji da kuma ƙoƙarin da ake na magance matsalar tsaro a ƙasar nan.
A wani labarin kuma Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Ɗan Sanda, Sun Bankawa Motar Sintiri Wuta
Wasu yan bindiga sun hallaka ɗan sanda guda ɗaya, sun ƙona motar sintirin yan sanda a jihar Delta.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar, Edafe Bright, ya tabbatar da kai harin, amma yace har yanzun suna gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng