Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi

Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi

- Shugaba Buhari ya yi jimamin mutuwar wadanda suka yi hadari a wani jirgin ruwa a jihar Kebbi

- Sanarwa daga fadar shugaban kasa ta bayyana yadda shugaban yaji, ya kuma taya iyalan wanda suka mutu jaje

- An ruwaito cewa, zuwa yanzu an fito gawarwakin mutane 5 da suka mutu a hadarin da ya faru a jihar ta Kebbi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin jirigin ruwa a jihar Kebbi, lamarin da ya bayyana a matsayin mummuna.

Shugaban wanda ya bayyana hakan a matsayin mummunan lamari, a cikin wata sanarwa ta hannun babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, The Nation ta ruwaito.

Shugaban ya yabawa wadanda ke ci gaba da aikin ceto tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan murmurewa cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce "Yayin da ake ci gaba da kokarin gano wasu da suka rage, Shugaban ya mika godiyarsa ga duk wadanda ke da hannu a kokarin ceto tare da yi wa wadanda suka samu rauni daga hatsarin fatan saurin murmurewa."

KU KARANTA: Bayan Amincewa Fulani Makiyaya Su Dawo Kano, 'Yan Sanda Sun Ba Da Sharadi

Shugaba Buhari Ya Shiga Jimami Da Jin Labarin Jirgin Ruwan da Ya Kife
Shugaba Buhari Ya Shiga Jimami Da Jin Labarin Jirgin Ruwan da Ya Kife Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

ukumar bayar da agajin gaggawa (SEMA) a jihar Kebbi ta ce an samo gawarwakin mutane 5 kawo yanzu daga cikin mutane fiye 160 da suka nutse a ruwa.

Lamarin ya faru ne yau Laraba da misali karfe 10 na safe, kuma bayanan da ke fitowa daga yankin na cewa kawo yanzu ana ƙoƙarin ceto waɗanda ya rutsa da su.

Bayanai dai na cewa jirgin ya taso ne daga Lokon Minna a jihar Neja zuwa garin Wara jihar ta Kebbi dauke da mutanen da suka hada da maza da mata da kananan yara, in ji BBC Hausa.

Amma sai ya rabe gida biyu ya kuma nutse tare da dukkan mutanen da ke cikinsa ana dab da isa garin na Wara.

KU KARANTA: Daliban Jami'ar Jihar Kaduna Sun Fita Zanga-Zanga Saboda Karin Kudin Makaranta

A wani labarin, Mahukunta a jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil a Jihar Kano ta ce za ta dauki "mummunan mataki" kan daliban da suka cin zarafin wata daliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata ta shafin Tuwita, shugaban sashen harkokin dalibai ya nemi afuwar dalibar sannan ya bukaci ta shigar da kara a hukumance domin neman hakkinta da aka take.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata daliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami'ar ne ta Wudil.

Asali: Legit.ng

Online view pixel