Daliban Jami'ar Jihar Kaduna Sun Fita Zanga-Zanga Saboda Karin Kudin Makaranta

Daliban Jami'ar Jihar Kaduna Sun Fita Zanga-Zanga Saboda Karin Kudin Makaranta

- Fusatattun daliban jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun fita zanga-zangar lumana a harabar makaranta

- Sun bayyana kokensu game da halin da suke ciki na karin kudin makaranta da gwamnatin jihar ta yi

- Sun bayyana cewa, tare da karin, 'ya'yan masu hannu da shuni ne kadai za su iya daukar nauyin karatu

Fusattatun dalibai a jami’ar jihar Kaduna (KASU) a ranar Laraba sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a babban harabar makarantar kan shirin da gwamnati ke yi na kara kudin makaranta daga N35,000 zuwa mafi karancin N150,000.

Daliban sun yi zargin cewa karin wani yunkuri ne na hana su hakkinsu na samun ilimi a matsayinsu na 'yan kasa, The Nation ta ruwaito.

Sun bayyana matakin da gwamna Nasir El-Rufai ya dauka a matsayin ganganci na kokarin sanya ilimi ya gagari 'ya'yan talakawa baya ga tuhumar kara kudin dakunan kwanan dalibai zuwa N80,000 da kuma korar iyayensu da za su ke daukar nauyinsu.

KU KARANTA: Hotuna da Bidiyon Yaron Da Ya Tashi a Daji Yana Cin Ciyawa Ya Ba Da Mamaki

Daliban Jami'ar Jihar Kaduna Sun Fita Zanga-Zanga Saboda Karin Kudin Makaranta
Daliban Jami'ar Jihar Kaduna Sun Fita Zanga-Zanga Saboda Karin Kudin Makaranta Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Daliban sun sanar da gwamnatin jihar cewa karin a wasu kwasa-kwasan zuwa N300,000 da N400,000 daga N36,000 zai tilastawa dalibai da yawa barin makaranta, in ji The Guardian.

Mista Abubakar Buhari, Shugaban kungiyar Daliban Kimiyya ta kasa, wanda ya yi magana a madadin daliban masu zanga-zanga, ya ce a baya kudin makaranta ya kasance tsakanin N24,000 zuwa N26,000 ga ’yan asalin jihar.

Buhari ya ce wadanda ba 'yan asalin jihar ba suna biyan tsakanin N31,000 zuwa 36,000, wanda ya danganta da fannin da suke karantawa.

Ya ce daliban sun yi matukar kaduwa lokacin da kafar makarantar ta nuna cewa ga sabbin dalibai, ‘yan asalin jiha yanzu za su biya N150, 000 a fannin zamantakewa da kuma N171, 000 a fannin ilimin kimiyya yayin da wadanda ba 'yan asalin jihar ba za su biya N221,000.

A cewarsa, fannin ilimin zamantakewar al'umma, 'yan asalin jihar za su biya N170, 000; wadanda ba ‘yan asalin jihar ba za su biya N200, 000 yayin da 'yan asalin jihar da aka ba su gurbin karatun likitanci za su biya N300,000 da N400,000 ga wadanda ba ‘yan asalin jihar ba.

“Muna yin zanga-zangar ne domin jawo hankalin gwamnatin jihar da ta koma kan tsohon farashi ko kuma ta rage kudaden ta yadda iyaye za su iya biya.

"Wannan kenan saboda yawancin dalibanmu da wahala suke iya biyan tsohon farashin kuma tare da wannan karin, 'ya'yan masu hannu da shuni ne kadai za su iya daukar nauyin ilimin jami'a a cikin makarantun jihar,'' in ji shi.

KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru

A wani labarin, Babbar jam`iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasiru El-Rufai da jefa makomar al`ummar jihar cikin hadari ta hanyar cin bashin da zai iya zama barazana ga al`ummomi masu tasowa.

Jam`iyyar PDP ta ce a cikin shekaru shida da suka wuce, gwamnatin APC mai mulki a jihar ta ci bashin da ya kai N170bn, kuma babu wani abin a zo a gani na wannan kudin.

PDP dai ta yi zargin cewa babu ranar biyan bashin amma tuni jam`iyyar APC ta musanta zargin. A cewar Manjo Yahaya Ibrahim Shunku mai ritaya, jigo a PDP ya bayyana wa BBC cewa gwamnatin El Rufa'i kadai ta karbi bashin $341m a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel