Wata Jami’a a Jihar Kano Za Ta Hukunta Wasu Dalibai Saboda Tsokanar 'Mai Abaya'

Wata Jami’a a Jihar Kano Za Ta Hukunta Wasu Dalibai Saboda Tsokanar 'Mai Abaya'

- Mahukunta a jami'ar Wudil sun bayyana daukar mataki kan daliban da suka ci zarafin wata daliba

- Wani bidiyo ya shahara a kafafen sada zumunta dake nuna daliban na cin zarafin wata daliba don ta sanya Abaya

- Hukumar makarantar ta ce sam ba ta amince ba, kuma lallai za ta dauki mummunan mataki akai nan kusa

Mahukunta a jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil a Jihar Kano ta ce za ta dauki "mummunan mataki" kan daliban da suka cin zarafin wata daliba saboda ta saka rigar abaya.

Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata ta shafin Tuwita, shugaban sashen harkokin dalibai ya nemi afuwar dalibar sannan ya bukaci ta shigar da kara a hukumance domin neman hakkinta da aka take.

A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata daliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami'ar ne ta Wudil.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Ci Bashin Da Ya Fi Karfin Kaduna, Ko Jikoki Ba Za Su Iya Biya Ba, Inji PDP

Wata Jami’a a Jihar Kano Za Ta Hukunta Wasu Daliba Saboda Cin Zarafin 'Mai Abaya'
Wata Jami’a a Jihar Kano Za Ta Hukunta Wasu Daliba Saboda Tsokanar 'Mai Abaya' Hoto: @Abdullahiabba
Asali: Twitter

"Hukumar Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Wudil ta samu korafe-korafe daga shafukan sada zumunta game da wata daliba da dalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya," a cewar sanarwar.

"Ni shugaban sashen harkokin dalibai zan dauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Dalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko daukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami'an tsaro."

Sanarwar ta ce abaya ba ta saba wa dokar saka tufafi ta jami'ar ba, "saboda haka dalibar ba ta karya wata doka ba".

KU KARANTA:

A wani labari, Fusattatun dalibai a jami’ar jihar Kaduna (KASU) a ranar Laraba sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a babban harabar makarantar kan shirin da gwamnati ke yi na kara kudin makaranta daga N35,000 zuwa mafi karancin N150,000.

Daliban sun yi zargin cewa karin wani yunkuri ne na hana su hakkinsu na samun ilimi a matsayinsu na 'yan kasa, The Nation ta ruwaito.

Sun bayyana matakin da gwamna Nasir El-Rufai ya dauka a matsayin ganganci na kokarin sanya ilimi ya gagari 'ya'yan talakawa baya ga tuhumar kara kudin dakunan kwanan dalibai zuwa N80,000 da kuma korar iyayensu da za su ke daukar nauyinsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel