Hotuna da Bidiyon Yaron Da Ya Tashi a Daji Yana Cin Ciyawa Ya Ba Da Mamaki
- Bidiyo da ke daukar lokacin da wani yaro mai nakasa ya isa wani birni kuma ya yi hulda da mutane ya bazu a ko'ina
- Kafin lokacin, yaron ya kasance yana rayuwa a cikin daji kuma yana cin ciyawa a matsayin abincinsa
- An nuna masa kauna da soyayya duk da cewa da yawa basu iya cewa komai sai dai mamaki da ta'ajibin lamarinsa
Wani yaron da ke da wata irin nakasa a karshe ya sadu da mutane kuma ya ga yankin birane a cikin bidiyo mai ban sha'awa da kwanan nan ya zagaye kafofin watsa labarai a yanar gizo.
Mai ba da labarin a cikin faifan bidiyon (@kingtundeednut) da ya yada a Instagram ya bayyana cewa kafin wannan lokacin yaron ya kasance yana zaune a cikin daji kuma yana cin ciyawa saboda kyama da mutane suke nuna masa.
Mahaifiyarsa mai karamin karfi ita ce kadai abokiyarsa yayin da ta dauki dukkan nauyin kula da shi duk da halin da yake ciki da kuma talaucinta.
KU KARANTA: 'Yan Najeriya Na Bukatar 'Yan Siyasa Masu Hankali, Gwajin Shan Kwayoyi Ya Zama Dole, NDLEA
Ya yi sa'a yayin da wata kungiyar taimakon agaji ta shigo cikin lamarinsa don taimaka masa tare da fitar dashi daga dajin.
A cikin faifan, mazauna birni sun shiga mamaki yayin da suke maraba da kuma hulda da shi.
Bai taba shigowa gari ba, don haka aka kai shi ya sami barci mai kyau a kan gado na alfarma, ya ci abinci mai kyau kuma a ka kai shi makarantar nakasassu.
Bidiyon ya sami martani yayin da ake yabon mahaifiyarsa saboda tsayawa kai da fata wajen ganin ta karfafa masa.
@keside_tmc ya rubuta:
"Wani abu da na koya daga wannan bidiyon shi ne, duk yadda mutane suka ga wannan yaron, mahaifiyarsa BA TA taba rasa kwarin gwiwa a kansa ba. Allah ya albarkaci dukkan iyaye mata a duniya."
@alumanu_yace:
"Mahaifiyarsa na matukar kaunarsa ... Na yi farin ciki da cewa mutanen kirki sun iya riskarsa."
@shopwithlizz.ng ya rubuta:
"Kai !!! A karshe ya bar mutane su matso kusa da shi. Ina matukar farin ciki da ganinsa yana hulda da mutane irin wannan. A karo na farko da na ga bidiyonsa, mutanen kauyensa sun sa shi bakin ciki saboda siffarsa kuma mahaifiyar ta yi alhini. Amma godiya ga Allah a kalla yanzu yana zagayawa cikin mutane."
KU KARANTA: Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Uzurin Buhari Na Kin Halartar Jana'izar Janar Attahiru
A wani labarin, A wani bincike da aka gudanar, an bayyana cewa ana gwada wata na'ura da aka rika sakawa a jikin Musulmai 'yan kabilar Uyghur domin gano yanayin bacin rai, kawa-zuci ko damuwarsu.
Wakilin BBC ya ce wani injiniyan manhajar na'ura wanda ya nemi a boye sunansa ya fadi cewa shi ya dasa na'urorin a ofishin 'yan sanda wadanda suke gano abin da mutum ke ji ko kuma yake tunani.
Ya ce ana amfani da na'urar wadda take gano sauye-sauye a jikin dan Adam wajen tantance laifin wanda ke tsare idan babu wata shaidar da ta nuna ya aikata laifi.
Asali: Legit.ng